LABARIN KARE DAN ALKAWARI

0

LABARIN KARE DAN ALKAWARI~~ Ya Shafe Shekaru 14 Yana Ziyartar Tashar da Uban Gidansa ke Hawa Mota.

Daga Abdulrahman Aliyu

Dangantaka tsakanin dabobi da mutane wani sannanne abu ne wanda har a cikin Alkura’ani an ambace ta. Dabobi suna da matukar sabo tsakaninsu da uwayen gidansu. Akwai tarihi da yawa da ya wanzu a duniya kan irin wadannan alakar tsakanin dabbobi da mutane.

Wannan labarin wani kare dan alkawari ne mai suna Fido, wanda wani wani magidanci ya tsince shi bayan ya samu rauniuka ya tafi da shi gidansa ya bashi magunguna har Allah ya sa ya samu sauki. Daga nan karen ya zamana duk inda mutumen za ya suna tare, shi ke raka sa ya je ya hau mota ya tafi wajen aiki, kuma in ya dawo zai je wajen hawa motar ya jira sa su tafo gida.

See also  SARKIN KATSINA IBRAHIM DAN MUHAMMADU BELLO

Wata rana wannan uban gidan nasa bai dawo ba, sakamakon kama shi da tawagar Borgo San Lorenzo suka yi a zamanin yakin duniya na biyu.

Haka wannan karen ya kwashe tsaqon shekaru goma sha hudu ya na ziyartar wajen da maigidansa ke hawa mota, wanda akalla sai da ya yi sawu sama da 5000 kullum sai yaje ko zai ga uban gidan nasa, amma shiru. Har dai mutane suka farga da shi, da kuma abin da yake zowa yi.

Wanda labarin wannan kare sai da ya zama abin kwatance a kasar Itali. Haka dai wannan kare ya mutu a bakin tashar motar nan yana jiran uban gidansa a ranar 9, Yulin shekarar 1958.

Daga karshe an yi butumbutunin karen nan a kasar Itali domin tunawa da irin kwazo da jarumtar da ya nuna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here