YARINYA ‘YAR SHEKARA 10 TA HAIHU A BENUWAI

0

YARINYA ‘YAR SHEKARA 10 TA HAIHU A BENUWAI:
DA MUSULMA CE DA YANZU DUNIYA TA CIKA DA KWARMATO

A jiya Litinin (5/08/2019), wata yarinya ‘yar shekara goma da hauhiwa, mai suna Masenengen Targbo ta haifi jaririya a wani asibiti da ke garin Makurdi na Jihar Benuwai.
*
Yarimyar, wacce aka tabbatar da cewa wani ne ya yi mata fyad’e kuma ta samu ciki duk da k’arancin shekarunta, an yi mata aikin fid’a ne aka ciro jaririyar da misalin k’arfe 1:00 na dare, a wani asibiti mai zaman kansa mai suna Foundation Hospital da ke garin na Makurdi. Jaririyar mai nauyin kilogiram 2:5 tana cikin k’oshin lafiya.
*
————————-
SHARHI/TSOKACI:
————————-
Wani abin mamaki da wannan al’amari a Najeriya shi ne, yadda manyan jaridun k’asar nan suka binne labarin a cikin jaridunsu, suka k’i ba shi muhimmanci sosai. Yanzu da a ce wata Musulma ce ta haihu a wannan k’arancin shekarun, na tabbata da yanzu ka ji ana kururuta labarin kamar duniya za ta tashi, koda kuwa a cikin aure ne yarinyar ta samu ciki.
*
Amma ga shi yarinya d’anya ‘yar shekara 10 ce kuma fyad’e aka yi mata, amma shiru kake ji kamar shirwa ta lamushe d’an tsako. Na tuna a kwanakin baya da Sanata #Ahmad_Sani_Yariman_Bakura ya auro wata yarinya ‘yar shekara 16 a k’asar Masar, babu cacar bakin da ba a yi ba a kafafen watsa labaran k’asar nan.
*
Wannan ya isa darasi ga al’ummar Musulmin Arewa su gane cewa lallai mu k’ara rik’e addininmu da k’arfi kuma mu gane cewa babu abin da ya kai aure da haihuwa muhimmanci. Da ake ta kururuwar kamfen, ana yak’i da auren wuri, ba don Allah ake yin haka ba, ana yi ne domin a lalata harkar aure da k’aruwar al’umma a cikin k’asarmu.
***

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here