0

WANI JIGO A JAM’IYYAR APC DAGA KARAMAR HUKUMAR RIMI YA BADA TALLAFIN SALLAH NA SAMA DA NAIRA MILIYAN BIYAR (#5′ 000,000).
=================================
Alh. Salisu Continental Jigo a jam’iyyar Apc dan asalin karamar hukumar Rimi ya raba sama da naira miliyan biyar (#5′ 000,000) don hidimar Sallah Babba mai zuwa. Da wasu gudumuwoyi don gyaran masallatai da islamiyyu.

Taron bada tallafin sallah anyi shi a garin Kadandani dake cikin karamar hukumar Rimi, wanda dan asalin garin ne na Kadandani. Hausawa na cewa kowa yabar gida, gida yabar shi, shiyasa duk lokacin da za yayi taro sai yaje gidansu kuma garinsu yayi taron don daratta asalin shi

Tallafin ba’a karamar hukumar Rimi ko garin Kadandani kadai ya tsaya ba abun ya shafi wasu bangarori na jihar katsina. Yakai taron gidan shi don daga daraja ta gidan shi, don asali shine cikar mutum.

Ga jerin yadda ya raba kayan…..!

(1) Masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Rimi (#500,000)

(2) Shugabannin jam’iyyar Apc na karamar hukumar Rimi tun daga matakin mazaba wards zuwa karamar hukuma (#1, 100,000)

(3) Ya bada atamfa guda (306) a raba ma mata na cikin karamar hukumar mazaba (wards) goma.

(4) Membobin kungiyar Manyan ma’aikata yan asalin karamar hukumar Rimi kowa atamfa guda (20) da (#100,00)

(5) Masu Makarantun Allo na cikin karamar hukumar (#350,000) su sayi naman sallah.

(6) Kungiyar Matasa masu hawan sallah na karamar hukumar Rimi (#50)

(7) Malaman makarantar pri, da cominiti sec. Na garin Kandandani Da santar kiwon lafiya ta garin Kadandani da cibiyar jami’an tsaro ta yan sanda dake garin Kadandani (#100,000)

(8) Ya Bada tallafin miliyan daya don gina dakin gwaje, gwaje LAB. a makarantar kominiti sec. Dake garin Kadandani.

(9) Ya Bada kyautar kekunan hawa guda goma ga Daliban makarantar Kominiti Sec. Kadandani da sukayi hazaka.

(10) Ya bada Sa namijin saniya guda daya ga ma’aikantan shi bangaren na’ura mai kwakwalwa da sauransu. Don suyi miyar sallah.

(11) Ya bada Sa Namijin Saniya guda daya ga ma’aikatan shi bangaren saye da sayarwa da motsa jiki GYM. Suma don suyi miyar sallah.

(12) Yaba Malamai Dattawa na Garin Kadandani (#100,000) su sayi naman sallah

(13) Komitin Darikar Tijjaniyya na unguwar Gabasawa Kwado ya basu gudumuwar (#100,000) don gina islamiyya.

(14) Kungiyar Izala Islamiyya Jos dake unguwar Makera kusada Airport ya basu gudumuwar (#100,000) don gyaran masallaci da islamiyya .

(15) Yaba kungiyar yan jarida reshen jihar katsina da suka buga littafi na ayyukan gwamnatin Apc a jihar Katsina daga 2015 zuwa 2019. (#250,000).

Wannan ba karamin kokari bane da nuna soyayya ga jam’iyyar Apc da Maigirma gwamna Aminu Bello Masari. Allah ya saka maka da alheri.

Shugaban jam’iyyar Apc na jihar Katsina Alh. Shitu S. Shitu shine Babban Bako na musanman kuma shine wakilin Maigirma gwamna a wurin taron. Mataimakin shugaban jam’iyyar Apc mai kulada shiyyar Katsina Alh. Mamman Yaro Batsari yana cikin mahalarta taron.

Sauran halartar taron sun hada da, Maza wajen Katsina Hon. Bilyaminu M. Rimi, Hon. Surajo Yazeed Abukur, Hon. Mu’azu Lemamu Tsagero, Alh. Aminu Chiroman kaura shine wanda ya wakilci Maigirma Kauran katsina. Dadai sauransu.

Report. Surajo yandaki.

Katsina State Apc Social Media Crew.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here