UWAR MARAYU, UWAR MARASA GATA, UWAR MARASA LAFIYA KUMA UWAR ‘YAN BIYU…

0

UWAR MARAYU, UWAR MARASA GATA, UWAR MARASA LAFIYA KUMA UWAR ‘YAN BIYU…

 


Mun Ciro daga shafin sarauniya na Facebook

Real Fauziyya D. Sulaiman bata bukatar gabatarwa, idan baka santa a rubutun Littattafan Hausa ba ba mamaki kana jin duriyarta a rubutun Fina-finan Hausa. Ko kuma ka taba cin karo da ita a gidan Talabijin na Arewa 24.

Idan ma duk baka santa a nan ba ta iyu ka santa a shafin sadarwa na zamani. Domin matukar za ka ga hoton talaka futuk cikin matsanancin rashin lafiya ana neman taimakon yi masa magani, da wahala ba aikin Fauziyya ba ne.

Idan ka ga hoton wata baiwar Allah cikin bakin talauci ga mugun ciwo ya mamaye ta ba gata sai Allah, duba da kyau zaka tarar Fauziyya ta riga kungiyar agajin gaggawa ko kungiyar kare hakkin mata zuwa wajenta.

Idan ka ga karamar yarinya ko yaro marayun da ba su ajiye ba kuma ba a ajiye musu ba basu kuma da inda zasu je sannan ga suna wani mawuyacin hali ana neman dauki, zaka tarar Fauziyya ta je ta magance komai ba tare da sanin Gwamnansu ko dan majalisa ko sanata ko kuma attajiran dake yankinsu ba.

Idan ka ga tsohuwa ko bazawara gidan ta ya zube an zube mata kayan aiki za a fara gyara ko an zube mata kayan abinci ta sa su a gaba tana rafsa kukan farin ciki, davwahala ba Fauziyya ce ta ziyarce ta ba.

Daga ina taimakon Marayu, Ina zuwa taimakon Marasa Lafiya, Kusan wannan shine aikinta da sauran wakilanta.

Mu Tallafawa Cibiyar Tallafawa Gajiyayyu da Marasa Lafiya ta Creative Helping Needy Foundation (CHNF) Da duk abinda za mu iya don Fauziyya ta ci gaba da taimakon Marayu, Marasa Lafiya da Marasa Gata, Shakka babu wannan aikin Alheri na da dimbin lada.

Taimaka ku sadaukar da fatar layyarku ga wannan Cibiya, Yanzu haka akwai jerin Marasa lafiyar da ke kan layin jiran kudin aiki ko na sayen magani.

Ga wadanda ke nesa za su iya Neman wakilanta ko ita su tura kudin fatar ta Asusun kungiyar.

Allah Ya yi riko da hannun UWAR ‘YAN BIYU.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here