0

MATASA DA SANA’ARSU: Sulaiman A. Tijjani (Farfesan Waka)

Tare da Abdulrahman Aliyu

A wannan makon cikin shirin Matasa da Sana’arsu Jaridar Taskar Labarai ta dira garin Kaduna inda ta gana da shahararren mawakin nan Sulaiman A Tijjani wanda aka fi sani da Farfesan Waka. Ya yi mana fashin baki kan yadda yaje gudanar da sana’arsa ta waka da rubutu da kuma irin nasarorin da ya samu tare da alfanun dake cikin wannan sana’a tasa.

Haka kyma ya yi kira ga matasa da su tashi tsaye su nemi nakansu domin dogaro da kansu su daina jiran gwamnati wajen basu aiki.

Ko shakka babu Farfesan waka gwamni ne a fagen waka kuma shahararre zamu kawo maku fashi bakin wasu wakokinsa a cikin filin Adabi da zamani da zai rika fita a duk ranar Juma’a. Ga dai yadda cikakkiyar hira tamu ta kasance.

Menene cikakken sunanka?

Sulaiman A. Tijjani, shi ne cikakken sunana an fi sani na da Farfesan Waka.

Ka bamu tarihinka a takaice?

Haifaffen garin Paki, karkashin Ikara Local Government, Kaduna State. Malam Ahmad Tijjani Adamu shi ne mahafina, na yi karatuna na Firamare da Sakandire duka a Paki. Kafin haka na yi karatun Tsangaya (Makarantar Allo) yayin da na kwashe kimanin shekara biyar zuwa shida bayan sauka biyu ta Alkur’ani da sauran littafan addini, sannan na dawo na ci gaba da karatun Sakandire a G.S.S Paki. Mun kamamala a shekara 2010, na nemi ci gaba da karatun Jami’a amma ba yiwu ba a wancan lokacin saboda takimar rayuwa da yanayin karatun kasar. Daga nan kuma ban hakura sai na ci gaba da bincike da karaence-karence domin kada d’abi’ar karatun ta gudu ta bar ni, saboda burina in zamo Farfesa a duk fannin da na tasa na karatu. Har gobe fatan kenan…

Yaushe ka fara wannan sana’ar?

Na fara sana’ar waka a shekara ta 2011 a karkashin kamfanin maigidanmu Alh. Rabiu Dalle wato Lafazee Entertainment.

Me da me kake gudanarwa wadda ya shafi wannan sana’ar?

Waka da kida. Wakokin fadakarwa da adabi su na fi yi domin
zaburarwa da tunatarwa saboda anfanin al’umma, sannan sauran wakoki kamar wakokin sarauta da na siyasa da wakokin biki da wakokin talla na kamfanoni ko sana’o’i da sauran su. sai kuma fannin rubuta labaran film wanda nake yi in adana saboda ina da burin ni ne zan yi amfanin da labaran da kaina; ma’ana ni zan shirya su da kaina.

Wace irin riba ka samu ta dalilin wannan sana’ar?

Alhamdulillahi! Masha Allahu… Ribar da na samu ko nake kan samu a dalilin wannan sana’a tawa ba za ta misaltu ba. Ribar farko ina jin dadi Allah ya ba ni sana’ar da nake baiwa al’umma gudummawa da ita, sai godiya. Saboda Annabi Sallahu Alaihi Wasallam ya ce mafi amfaninku wanda ya fi amfanar da mutane. Daga cikin ribata a wannan sana’ar a baya a karkashin wani nake aiki yau kuwa ina da kamfanina na kaina wanda ni ne C.E.O/MD wato Farfesan Waka International, wanda kuma masu cin abinci a karkashin wannan kamfanin Allah ya yi yawa da su. Duk wata ni’imar rayuwa kuma da Allah ya yi ake iya gain sandin wannan sana’a ne. Sauran abubuwan da aka mallaka kuwa a dalilin wannan sana’a sirri ne…

Ya kake ji yanzu a rayuwarka matsayinka na mai dogaro da kansa?

Ina jin dadi kuma ina matukar alfahari da hakan saboda. Kuma a yadda nake yanzu na fi ji na a natse fiye da in da ina karkashin wani ne. Domin babu abin farinciki kamar a ce kana rayuwa ne bisa tsarinka da manufofinka ban a wani ba. Na wani ko da ba su dace ba kuma ba su yi maka amma haka za ka rayu das u saboda a karkashinsa kake. Akwai dadi ka dogara da kanka!

Wace shawara zaka ba matasa domin su rungumi sana’a wadda zasu dogara da kansu?

Kowa yana yin aiki ne domin ya samu abin dogaro da kai sannan ya rayu, amma shi mai dogaro da kai rayuwar kawai zai yi domin ya rigaya ya dogara da kansa tun farko. Matasa dole kowa ya tashi ya kama sana’a saboda in ma ba ka bukatar komai to kana bukatar abinci da lafiya, dukansu kumai sai da kudi, ina za a sami kudi sai da sana’a.
Ba ni jin dadi in ga matasa wai suna jiran aiki mai tsoka ga wadanda suka yi karatu wadanda bas u yi ba kuma suna kyamatar wasu sana’o’I saboda ba a samin garabasa a cikinsu sai an yi aiki tukuru. Matasa mu ne manyan gobe dole a rage kasala da lalaci da sakarci da banbadanci domin rayuwa ta yi kyau. Duk abin da ka tasa ba ka yi nasara ba ka bar abu hudu: Juriya da kwazo da naci da hakuri. In dai ka hada wadan nan abubuwan akan kowace sana’a kake sai ka zama wani a kan ta.

Daga cikin manya darusa guda shida da a ka fitar a cikin littafin Rich Dad Poor Dad na Robert Kiyosaki tare da Sharon Lechter, ina yawan tuna guda biyu kuma suna zaburar da ni tare da cire min kasala. Darasin dake nuni da cewa kullun mutum ya dubi rayuwa ta fuskar yawon damammakin cikin wannan rayuwa, abin da Bahaushe kan cewa, idan hagu ta kiya a koma dama. Sai kuma darasin da ke nuni da cewa, tsoro da rashin yadda da kai ko kokwanta kwazo su ne gagaruman tarnakan da kan tadiye nasarar Dan’Adam. Duk abin da ka tasa ka yi kwazo ka rungumi abin nan sai ya rungume ka shi ma, ma’ana ka yi shi domin ka yarda za ka iya… Ka cire tunanin na yi–na yi ya ki yiwuwa, zai yiwu!
Matasa su daina raina sana’a komai kankantarta domin ta fi zaman banza, kuma da rarrafe yaro ke tashi.

Wadanne wakoki ne kake alfahari da su?’

Duka wakokina ina alfahari da su musamman Kurman Baki da Mayan Arewa Dakon Gulma da Bahaushen Girka da Alkalai da Bawan Zuciya da Tsawon Dare.

Jaridar Taskar Labari na maka godiya da fatan Alheri.

A madadin kamfanin Farfesan Waka International, muna godiya kwarai.

Zaku iya neman Farfesan Waka ta akwatin email dinsa kamar haka: farfesanwaka@gmail.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here