BARAYIN DAJI SUN KAI HARI A BATSARI

0

BARAYIN DAJI SUN KAI HARI A BATSARI

Daga Lawal Iliya Batsari

@Taskar Labarai $ the links news

Alokacin da al’ummar karamar hukumar Batsari dake jahar Katsina suka fara murna da farinciki sakamakon lafawar hareharen ‘yan bindiga da barayin shanu a yankunansu, tun daga lokacin da gwamnatin jihar Katsina tayi sanarwar sasanci da barayin shanu, tun daga lokacin aka daina jin karar bindiga kojin labarin mamaye gari.

Amma ga alama murna na neman komawa ciki domin a
jiya asabar 10/8/2019 tun misalin karfe 11pm na dare barayin shanu suka mamaye Kandawa basu fita ba sai zuwa 6:am na safe, inda suka sace duk wani abu mai amfani kama da shanu, tumaki, raguna, babura da kayan shaguna, a kalla
sun sace daruruwan dabbobi da baburan hawa sama da 100, bayan sun kashe mutum daya mai suna SHAWWAL.

Har sukayi abinda suka yi babu wani dauki daga jami’an tsaro duk da an sanar dasu halinda ake ciki. Kafin wannan zuwan na kandawa a ranar alhamis 8/8/2019 na safe
barayin sun tare motoci 2 dauke da shanu sama da 20 inda suka yi awon gaba dasu tare dayin garkuwa da mutum daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here