Gwamnatin Kano Ta Umarci Duk Hakimai Su Yi Hawan Daushe A Masarautunsu

0

Sanarwa Daga Gwamnatin Jihar Kano!

Bikin Sallah : Gwamnatin Kano Ta Umarci Duk Hakimai Su Yi Hawan Daushe A Masarautunsu

Sabanin wani labari da yake ta yaduwa a kafafen sadarwa na zamani cewar wai a na gayyatar Hakimai gaba dayansu da su je Hawan Daushe a fadar Sarkin Kano, Gwamnatin Jihar Kano ta UMARCI DUKKAN HAKIMAI DA KOWANNENSU YA JE HAWAN DAUSHE A MASARAUTARSA.

Umarnin ya yi bayanin cewa an umarci dukkan Hakiman da ke karkashin Masarautar Kano da su je Hawan Daushe a masarautar Kano din. Dukkan Hakiman da ke karkashin Masarautar Bichi, da su je Hawan Daushe tare da Sarkinsu mai daraja ta daya Alhaji Aminu Ado Bayero.

Haka nan an umarci dukkanin Hakiman da ke Masarautar Rano da su je Hawan Daushe tare da Sarkinsu mai daraja ta daya Alhaji Dakta Tafida Abubakar (Autan Bawo).

An kuma umarci Hakiman da ke Masarautar Karaye, da su je Hawan Daushe tare da Sarkinsu mai daraja ta daya Alhaji Dakta Ibrahim Abubakar II. Sai kuma Hakiman da ke Masarautar Gaya an umarce su da su je Hawan Daushe tare da Sarkinsu mai daraja ta daya Alhaji Ibrahim Abdulkadir.

Gwamnatin ta na taya jama’a bikin babbar Sallah. Tare kuma da fatan za a yi dukkan bukukuwan Sallah lafiya cikin kwanciyar hankali. Yayin da gwamnati ta tanadi dukkanin matakan da za su kawo tsaro mai inganci a lokutan bukukuwan Sallar nan.

Abba Anwar
Babban Sakataren Yada Labaran Gwamnan Jihar Kano
Lahadi 11 ga Watan Agusta, 2019

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here