RIKAKKEN DAN TADDA : ALHAJI HAMISU BALA WADUME.
daga Shafin Datti assalafi
Wannan shine Alhaji Hamisu Bala Wadume, rikakken ‘dan ta’adda, shugaban masu garkuwa da mutane na jihar Taraba, wanda yayi sanadin hallakar kwararrun jami’an ‘yan sandan Nigeria guda uku da suke aiki da rundinar IGP-IRT karkashin jagorancin DCP Abba Kyari
Jaridar Vanguard ta wallafa wani sabon rahoto da ta tattara akan abinda ya sa wasu gurbatattun sojoji suka hallaka ‘yan sandan guda uku da farar hula guda daya, bayan da ‘yan sandan suka kama wannan gawarutaccen shugaban masu garkuwa da mutane
Rahoton yace tuni rundinar sojin Nigeria ta cafke jami’in soja mai mukamin Kyaftin wanda ya bada umarni wa kananun sojoji suka kaddamar da harin kwanton bauna wa jaruman ‘yan sandan, an kamashi ana gudanar da bincike
Sannan shi wannan kasurgumin ‘dan ta’adda ana zargin ya sayawa Kyaftin din sabuwar mota, ance duk wanda aka tura gurin yana saya musu motoci, kasancewar ya tara makudan kudi a harkan garkuwa da mutane da yake yi
Bayan haka, gurin da jami’an tsaro suke shan giya shi yake biyan kudin don ya samu aminci da kariya daga gurin jami’an tsaron gwamnati akan mummunan sana’ar da yake yi, hatta matasan yankinsa yana taimaka musu da irin kudaden da yake samu ta haramtacciyar hanya, don har ya taba tsayawa takara yana neman kujeran ‘dan majalisar jiha
Sannan dazun nan Maimagana da yawun shugaban kasa Buhari Malam Garba Shehu na ga ya fitar da sanarwa akan wannan abinda ya faru, Malam Garba Shehu yace shugaba Buhari ya dauki lamarin da gaske, saboda shima abin ya bata masa rai, kuma ba zaiyi sassauci ga duk wanda aka samu da hannu cikin salwantar da rayukan kwararrun jami’an ‘yan sandan ba
Malam Garba Shehu yana mayar da raddi ne ga wadanda suke cewa shugaba Buhari yana sanyi akan wanann cin amanar tsaron Nigeria da ya faru
Sakamakon wannan abindaya faru ya fusata zukatan ‘yan sanda kwarai da gaske, don ko a jiya na ga signal da rundinar sojin Nigeria ta rabawa jami’anta akan wannan batun ana gargadinsu da su kyautata mu’amalarsu da ‘yan sanda, sannan su guji tafiya da kakin sojia gurin da akwai ‘yan sanda, signal din yana nan yana yawo har a jaridu
Bayan wannan, akwai sanarwan da Maigirma kwamishinan ‘yan sanda na jihar Taraba ya fitar yake gargadin jami’an ‘yan sanda da suke aiki a jihar da su shiga taitayinsu, kar su kuskura suyi wata tattaunawa da kowa face da izninsa, kar su kuskura su bar wani jami’in tsaro ya shiga farfajiyar ofishinsu, saboda bayan da sojoji suka hallaka ‘yan sandan, don su boye cin amanar tsaron kasa da sukayi, sai suka je ofishin ‘yan sanda na garin Ibbi suka tarar da wani sokon ‘dan sanda suna masa tambayoyi akan ko ya san da zuwan dakarun IRT? shi kuma da yake soko ne sai ya bada amsa, alhali bai sani ba suna recording dinsa, sunyi haka ne don su boye gaskiya
Wannan abinda ya faru ya jawo yanzu haka mutanen da suke kusa da inda abin ya faru sun fice sun gudu saboda tsoron abinda zai biyo baya, shi kuma ‘dan ta’addan da sojojin suka kubutar ya gudu, har yanzu babu labarin inda yake, dakarun ‘yan sanda suna nan sun bazama a dazukan jihar Taraba suna nemanshi dare da rana safe da yamma, kuma muna masu tabbatar muku da cewa sai ya fado hannu da taimakon Allah
Tabbas wannan abin ya girgiza zuciyar duk wani mai kaunar zaman lafiya a Nigeria, muna kyautata tsammanin Allah Madaukakin Sarki Zai yi amfani da jinanen wadannan kwararrun jami’an ‘yan sandan ne ya tona asirin cin amanar tsaron kasarmu Nigeria da aka jima ana yi, ba abinda maciya amanar tsaron suka iya sai dai kisa da barazana don su boye gaskiya, wannan karon gaskiyar ba zata boyu ba da taimakon Allah Maji rokon bayinShi
Allah Ka bayyana gaskiya don Karfin Izza da BuwayarKa