WANNAN ITA CE GAIWA

0
1070

WANNAN ITA CE GAIWA…..

Rabiu Biyora

Gaiwa wata halitta ce dake rayuwa a cikin ruwa, tana kama da TARWADA a siffa, amma halayyarta daban take….

A zahiri zaa ga kamar tana da hakuri da rashin son fitina, sai dai takan kasance cikin damuwada tashin hankali a duk lokacin da taga wata yar’uwarta GAIWA na neman yin abun kirki…

GAIWOWI sukan taru su cinye duk GAIWAR da sukaga alamun daukaka ya bayyana gareta, duk da cewa GAIWA tana haifar ya’ya masu yawa, sai dai bata da abuncin daya wuce ya’yanta ko ya’yan wata Gaiwar wanda hakan yasa rayuwar GAIWA take kasancewa kuntacecciya….

A wajen Gaiwa da yar uwarta taci gaba har tayi girma, gwara ya’yan Tarwada su girma, ita nata ne kawai bataso…..

Sanin halayyar GAIWA hakan yasa Malam Aminu Kano ya dade yana kiran mutanen Arewa musammam talakawa akan su gujewa kwaikwayon rayuwar GAIWA….

Amma da dukkan alamu, a yanzu mun kwarance a kalar rayuwar GAIWA, da wahala kaga namu yana kaunar namu, burinmu namu ya karye don kawai bamu bane, gani muke kamar gwara bayerabe ko Inyamuri yayi gwaninta maimakon namu yayi….

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here