GODIYA GA MAI MARTABA SARKIN BICHI

0

GODIYA GA MAI MARTABA SARKIN BICHI

Babba Aminu Ado Na wa.

Title nake nufi na sarauta,
banso ya shafi harkar Waka

Domin sarautaka kan Waka,
Allah ka basuwa ba shakka

Aikin mutum ake dubawa,
sai Jama’a su shasshaida ka

Waka ita take nada sarki,
don kanta babu dangantaka

Waka irin ta harshen Hausa,
ga doki ga fagen sukuwa!

Zuwa yanzu ina zaton da dama za su fahimci wannan baitin wakar na ‘DAN’AMANAR BICHI.

A ina da ina ka taba ganin Sarautar Sarkin Waka ta yi tasiri. Kamar yadda ya fadi waka ita ke nada Sarkin ta da kanta. Mu koma kan Mahadi mai dogon Zamani. Alhaji Dr Mamman Shata babu wani Basarake ko Masarauta da ta taba cewa ta Nada shi Sarkin waka. Babu wani taro da aka yi cewa ga shi yau shine Sarkin Waka na kasar Hausa, amma waka ta yi ma sa nadin da ko Giyar wake mutum ke sha ya San Shata Sarkin Mawaka ne. A zamanin Shata ka na ganin sa ba sai an fadi ba kasan Sarki ne. Idan Shata ya zo waje dole Mawaka su yi Saranda ga uban su kuma sarkin su ya zo. Waka ta yi Shata nadin da ya fi wani Basaraken, waka ta yiwa Shata nadin da ya fi wani mai mulkin, waka ta yiwa Shata nadin da ya fi wani mai arzikin. Duk Sarauta duk mulki kuma duk dukiyar Mutum ba zai keta ko wulakanta Shata ba.
Mu ajiye duk wannan a gefe. Mawaka nawa su ka yiwa Dr Mamman Shata waka. Wannan kadai ya isa nunawa Jamaa cewa lallai waka ta yiwa Dr nadin Gaske,nadin fusaha da zalaka da Basira.

A fahimtata da zamana da kuma Nazarina da Mawaka, ba sa amince da mutum Sarkin su ne sai sun yarda lallai Fusahar sa ta kai, sai sun amince da kaifin Basira da Zalakar sa. Ko Dr Mamman Shata akwai Mawakan da su ka yi ta ja da shi a wancan Zamanin. Su na ja da shi ne saboda Dan adamtaka ba wai don su na ganin bai fi su ba. A wata hira ta Marigayi Alhaji Amadu Doka ya fadi cewa sun Ja da Shata amma wallahi Shata fasihi ne, kuma su na sauraren Wakokin sa domin su Debi fusaha da Salo. Alhaji Musa Dan Bade ya sa fadi da jinjina fusahar Shata duk da ya yi wakokin da ake ganin Kamar zambo ya ke yiwa Shata.

Mu da ke tare da Alhaji Aminu Alanwaka ‘DAN’AMANAR BICHI. Mun sani da dadewa bai ko kusa da son wata Sarauta da ta Shafi waka, Kamar yadda ya fadi shekaru ma su yawa da su ka wuce a baitin Waka. Shi a dabia ba mutum ne mai son Jagoranci ba. Ya na ganin Kamar wata Sarauta da ta shafi waka za ta hada shi fada da Yan uwansa Mawaka ko kuma ya zama bai da sakewa ga gabatar da al’amuran sa na yau ga kullum.

Ni kuma a tawa fahimtar, Sarautar Sarkin Waka ba ta da wani tasiri da muhimmanci. Na farko duk wani nadin da aka yiwa wani a matsayin Sarkin waka bai da tasiri, domin babu wasu mawaka Wanda zai mulka da wannan Sarautar matukar ba waka CE ta yi ma sa nadi Kamar yadda ta yiwa Shata ba.

Ko ba’a tambaya ba, Sarautar ‘DAN’AMANAR BICHI da Mai Martaba Magajin Dabo Sarkin BICHI Alhaji Aminu Ado Bayero yai wa Alhaji Aminu Ala , ya yi ya ne Saboda Yadda Alanwaka ya rike Amana da Zumuncin Kauna dake tsakanin sa da Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Abdullahi Bayero Allah ya gafarta ma sa.
Ya rike kauna da zumunci tsakanin sa da ‘Ya’Ya da Jikokin Mai Martaba San Kano. Ya rike Kauna bisa Soyayya da Amana. Ya rike kauna irin wacce ke karkashin zuciya ba domin wasu kyale kyale na alatun duniya ba.
Mu da ke tare da shi mun San tsantsar kaunar da ke tsakanin sa da takawa da Ahlinsa, kuma mun San irin yadda duk wani tsatso na Takawa ke nunawa Alhaji Aminu Alanwaka kauna.

A madadin Abokai da Yan uwan ‘DAN’AMANAR BICHI Alhaji Aminu Ladan Abubakar Alanwaka. Muna mika Godiya da Ban girma ga Amir BICHI Mai Martaba Alhaji Aminu Ado Bayero. Bisa wannan Sarauta ta ‘Dan’amanar BICHI da ya ba Alhaji Aminu Ladan Abubakar Alanwaka.

Allah ya taimaki Sarki ya daukaka shi ya kare shi daga Sharrin Makiya. Allah ya zama gatan Mai Martaba a duk wajen da ya kasance.

Auwal Garba Danborno Kano.
A madadin Abokai da Yan uwan Dan Amanar BICHI.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here