YADDA BARAYIN SHANU SUKA KAI HARI RUMA

0

YADDA BARAYIN SHANU SUKA KAI HARI RUMA
Daga lawal iliyasu batsari
@ taskar labarai & the links news

Tun da misalin karfe 10:30 na daren Litinin ne 12/8/2019, Barayin shanu dauke da miyagun makamai suka mamaye garin Ruma dake cikin karamar hukumar Batsari dake Jihar Katsina, Inda suka kama harbi kan mai uwa da wabi tare da shiga cikin gidajen jama’a suna yin awon gaba da duk wani abu mai amfani, sun harbi mutum 6, daya daga cikinsu ya mutu nan take mai suna Nasiru Ojo, 5 na asibiti.
1 Abu Karfe,
2 Amadu Hasan
3 Ali Dan asibi
4 Shamsu Ya’u
5 Abu Danjari

Sunyi garkuwa da mata 12, tare da namiji daya mai suna uzairu basiru, Danshekaru 13,
.

daga karshe dai sojoji sun kawo dauki bayan maharan sun gama aika-aikarsu jama’ar gari dai sun yi wa sojoji ihu bayan fusatar da sukayi ganin babu wata tazara tsakanin garin na Ruma da Batsari, domin bazai
wuce kilo Mirt 12, ba. Amma sukaki zuwa har sai da maharan suka gama ta’addancinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here