SARKIN DAURA YA KARA AURE?

0

SARKIN DAURA YA KARA AURE?

Daga Taskar Labarai


Ana yadawa a kafar sadarwar zamani cewa, mai martaba sarkin Daura Alhaji Umar Faruk Umar CON ya kara aure, wai ya auri wata bazawara mai suna Lubabatu Bala Kankanba.

Bincike da jaridar Taskar Labarai tayi ta gano wannan labarin karya ne, sarkin Daura bai kara wani sabon aure ba.

Taskar Labarai ta gano cewa, ita Lubabatu Bala Kankanba tsohuwar matar wani dan sanda ne mai suna Garzalai Ahmad wanda har ya kai matsayin kwamishinan ‘yan sanda ya rasu bayan wata rashin lafiya.

Lubabatu tana da ‘ya’ya guda uku da Garzali mata biyu namiji daya, mahaifinta shi ne Alhaji Bala Kankanba mahaifiyarta kuma Ba’azbina ce ‘yar kasar Nijar.

Bincikenmu ya tabbatar mana da cewa Lubabatu ita ta kawo kanta ga sarkin Daura tana neman aure ta, har sallar da ta gabata ta kwaso danginta suka zo Daura kallon sallah.

Bincikenmu ya tabbatar mana cewa har gidan sarkin Daura ta je don gaida uwargidansa, kuma ta bayyana mata cewa tana son sarkin Daura da aure.

Taskar Labarai ta gano wannan son auren sarkin Daura da ya ruda Lubabatu sai kawai ta rika gayawa duk wanda zai saurare ta cewa zata auri sarkin Daura da sallah.

Da aka yi sallah aka ji shiru ana zargin wasu na kusa da ita da suka fara yada cewa ai an ma yi auren.

Bincikenmu ya tabbatar da cewa, duk wannan barankidama da Lubabatu ke yi ita kadai ke kidanta kuma take rawarta. Ba wata maganar aure tsakanin ta da sarkin Daura, balle har ai wani shiri akan aurenta.

Don haka labarin sarkin Daura ya kara aure karya ce, tsagwaronta, babu ko kamshin gaskiya a cikin ta.
________________________________________
Taskar Labarai jarida ce mai zaman kanta da ke bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com da kuma sauran shafukan sada zumunta da layin kira ko WhatsApp na 07043777779. Tana da yar uwarta ta Turanci mai suna The Links News dake a www.thelinksnews.com da layin waya ko WhatsApp 08020570059

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here