BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA MAI GIRMA GWAMNAN JAHAR KATSINA AMINU BELLO MASARI ~~Karo na 5
Assalamu Alaikum warahamatullahi wabarakatuhu,
Mai girma gwamna,
KAYAN GWAMNATI SUN ZAMA ABIN WASOSO GA WADANSU A UNGUWAR KWADO?
Kamar yadda kake gani a sama, hotunan wani filine na Firamarin unguwar mu (unguwar kwado bayan ma’aikatar Alhazai kan hanyar Daura) wanda wasu makiya gwamnatinka suke so su cinye, har sun kusan kammala harabar filayen,
Mai girma gwamna, abin ya samo asali ne tun a gwamnatin PDP, bayan wannan gwamnati ta turo a yiwa makarantar haraba, sai wasu bara-gurbi suka yi amfani da wannan damar suka fidda wadannan filaye da kake gani daga cikin harabar makarantar, suka rabawa kansu, shi ne yanzu suke ginawa.
Abin ya farune kusan shekara 6, ko 7 da suka gabata kafin hawan wannan gwamnati mai albarka. A lokacin manyan wannan unguwa mai albarka (elders) hadi da masu unguwanninmu suka hadu su kace ba zasu yarda ba, wanda haka yasa suka rubuta koke (petition) suka kai( LEA), tare da bin diddiqin takardar wanda hakan yasa dole aka tsaida aikin fandeshar da suka fara a wancen lokacin, wannan yasa shuwagabannin wannan unguwa tamu suka natsu akan cewa an hanasu yi ne.
Ashe basu daddaraba, ashe bakam sukai, abin mamaki sai gashi bayan wadannan shekarun kwatsam muka wayi gari mukaga an cigaba da ginin wannan guri, yau kusan kwana 14 da fara ginin kamar yadda kake gani.
Da elders namu da masu unguwanni suka ga haka sai suka dunguma sukaje LEA kwanaki 9 dasuka wuce dan suji ya akai aka cigaba da wannan haramtaccen aiki?
Abinda aka gaya masu shi ne, “wannan fili an saida shi kuma har masu shi anbasu certificate”.
Abin mamaki, waya saida filin? Waya basu shaidar mallakar? (certificate of occupancy) da sanin gwamnati abin ya faru koko so ake a bata mata suna a idon mutanen Kwado da Kambarawa ne? Tabbas muna da bukatar amsar wadannan tambayoyin.
Domin bamu tsammani aikin da har aka iya dakatar da shi a lokacin PDP ace kuma wannan gwamnatin tabari an cigaba da yinsa.
Maigirma gwamna, muna so, kasa aje LEA a gudanar da bincike a zakulo takardar da muka kai ta koke a gani a wadancan shekaru da suka gabata, domin duk takardun da muka rubuta muna da copys nasu aje, ba LEA kadai muka kaiwa takarduba na dai ambaci LEA ne kadai saboda kai tsaye abin ita ya shafa domin ana butun ilimine (EDUCATION)
Domin maigirma, Gwamna asali ba wannan filin ne kadai ake kokarin cinye wa ba.
Tarihi bazai manta da cewa a lokacin Mulkin PDP lokacin da aka maida tsohuwar (NRC building) a matsayin hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar Katsina (Pilgrimage welfare Board) lokacin ne aka debe kusan kashi daya bisa ukkuna filin primary din akayi gine-gine, kaga wannan gwamnati ce tayi kuma ma’aikatar gwamnatice aka yi, bamu da matsala da hakan.
Amma abin mamaki sai jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki na wancan lokacin sukayi wasoson kashi daya bisa biyun da yarage wajen 600× 200 fits.
Sai suka bar sauran kashi daya, wanda a cikin sa ne ginin wannan makarantar yake, shima a wancan lokacin sai da elders namu sukai ta bibiya da rubuce-rubuce, amma da yake lokacin tsurar PDP ke mulki ko kallo basu ishesuba balle aji koken su, suka gaji suka bari, to wannan ma ta wuce domin bayadda muka iya.
To sai kuma suka kirkiri yima sauran kashi dayan haraba kamar yadda na fada, kuma sukai wancan aika-aikar.
Maigirma gwamna, abinda mu keso shi ne ka taimaka mana wannan sauran fili da suke kokarin ginewa a hanasu a maidawa makarantar filinta.
‘Yan unguwar kwado community su yanke shawarar abin da za suyi dashi tinda an riga an harabance makarantar,
Domin wallahi-wallahi mun shirya tsaf da fuskantar wannan batu a hukumance tinda ga gwamnatin jaha har ta tarayya, mun riga mun tsara (Drafting letter ) tana nan za muyi (copy)
CC To Daily Trust Newspaper,
CC to EFCC,
da sauran news papers.
Ya zuwa yanzu abu daya muke jira shi ne:-
A sakamakon rubuce-rubuce da mu kai a wannan kafa ta FB, akwai wani bawan Allah daya nememu yace shi yana kusa da maigirma gwamna zai kai kokenmu gunsa shi ya sa muka dakata, shi ma ‘yan kwanaki muka bashi, idan mun ga akwai cigaba to muna murna, In kuma munga babu to zamu cigaba da wannan yakin.
Saboda haka inda gaske yake to muna ba mai girma gwamna shawarar cewa irin wadannan mutanen abin rikewane ka rikekeshi, domin ya nuna mana damuwarsa sosai akan ana sone kawai a batawa gwamnatinka suna ne.
Mun gode maigirma gwamna,
Hamisu Abdulmumini Kwado,
Daura road bayan masallacin juma’a na Jabir bn Abdullahi,
A madadin kunyar rajin kawo cigaban al’ummar mutanen Kwado (Kwado Community Development Forum).