Ko ka san tsayin jijiyoyin jinin jikinka zai iya zagaye da’irar duniya har fiye da sau biyu?

0

Allah Gwani: Ko ka san tsayin jijiyoyin jinin jikinka zai iya zagaye da’irar duniya har fiye da sau biyu?
____________________

Jijiyoyin jini ƙananan hanyoyi ne da jini ke bi yayin da ya ɗauko iskar oksijin da sinadaran abinci daga zuciya zuwa dukkan sassan jiki, sannan su ɗauko gurɓatacciyar iskar “kabondai oksayid” da sauran gurɓatattun sinadaran da jiki ba ya buƙata zuwa zuciya da sauran sassan jiki.

Bincike ya nuna cewa idan da za a warware ko a miƙar da waɗannan jijiyoyin jini gaba ɗaya, tsayinsu ya kai Mil dubu sittin (kimanin Kilomita dubu ɗari kenan), saboda haka tsayin jijiyoyin jinin zai iya zagaye ƙwallon duniya fiye da sau biyu da take da faɗin da’ira kimanin Mil dubu ashirin da biyar.

#Angiogenesis
#Anastomosis
#BloodVesselsNetwork

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here