Allah Gwani | Abubuwan ban mamaki goma dangane da zuciya.
_______________________
1] Zuciya tana fara bugawa tun kwanaki 22—23 da halittar ɗan-tayi a mahaifa.
2] Girman zuciyar mutum ya kai girman dunƙulallen hannun mutum.
3] Zuciya tana bugawa sau 60—100 a minti ɗaya yayin hutu — yayin da ba’a aiki.
4] Zuciya tana bugawa kimanin sau dubu ɗari (100,000) a kowacce rana.
5] Zuciya tana buga ko harba jini da ya kai yawan galan dubu biyu a kowacce rana.
6] Zuciya tana iya cigaba da bugawa bayan an cire ta daga jiki.
7] Zuciya ta dogara ne da tsarin lantarki domin bugawa.
8] Jarirai na da bugun zuciya mafi sauri da ya kai bugu 70 —190 a minti ɗaya.
9] Zuciya tana harba jini zuwa jijiyoyin jinin da tsayinsu ya kai mil dubu sittin (60,000 Miles) in da za’a warware su.
10] An fara yin tiyatar zuciya a shekarar 1893, wanda likitan zuciya Daniel Hale Williams baƙar fata ɗan ƙasar Amurka ya gudanar.