Jirgi Mai Saukar Angulu Ke Kawo Mana Bindigogi A Dajin Kankara,

0

Jirgi Mai Saukar Angulu (Helicopter) Ke Kawo Mana Bindigogi A Dajin Kankara, Cewar Yaron ‘Yan Bindiga Aliyu Musa

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina, ta yi nasarar Kama wani yaron barayin shanu, Mai suna Aliyu Musa, dan shekara ashirin da haihuwa da ke Chediya a cikin Karamar Hukumar Kankara a jihar Katsina.

Musa ya bayyana wa manema labarai, a helkwatar rundunar da ke Katsina, cewa “tun ina dan karamina, wani Bafullatani wanda ake Kira Oga Surajo ya dauke ni, ya kai ni dajin Dinya, domin yi masa kiwon shanu, daga nan sai ya fara gayyata ta zuwa shatar shanu, da balle shagunan mutanen gari, mu ke korar shanun da aka sato da Kuma kashe mutane” cewarsa

Da aka tambaye shi Ina su ke samun makamai da suke gudanar da wannan aika-aika sai ya kada baki ya ce “ni dai tsakani da Allah ni dai a gaban idona, jirgi ya zo da kamar igiyar shanun nan, sai ya tsaya tsaye a sama, sai oganmu Surajo ai ta sakko Masa bindigogi daga saman jirgin, shi Kuma Suraj na kwankwancewa kuma bindigun sun fi ashirin. Jirgin fari ne Mai falfela da yake zuwa dajin Dinya a Kankara kuma da rana ya ke zuwa dajin” in ji shi

A ranar 15, ga wannan watan da muke ciki aka Kama su, sakamakon bayanan sirri da muka samu, mun cafke Salmanu Isa da ya fito a kauyen Danbago da Kuma Aliyu Musa daga kauyen Chediya dake Karamar Hukumar Kankara. Kuma su ne ke kai a Karamar Hukumar ta Kankara. Cewa ASP Anas Gezawa kakakin rundunar ta jihar Katsina.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here