LABARIN MAI GARKUWA DA MUTANE A TARABA:
Daga Bello Muhammad Sharada.
CIKAKKEN sunansa, Hamisu Bala, ana kiran inkiyarsa Wadume. Shekararsa 32. Dan karamar Hukumar Ibbi ne a jihar Taraba. Yana da mata hudu. Yan kwanaki kadan suka rage Sarkin Ibbi ya ba shi sarautar Sarkin Matasa. Yana jin harshen Hausa da Fulfulde. Mutane sun nemi ya tsaya takarar Majalisar jiha a jam’iyyar YDP amma bai yi nasara ba.
A kaf Garin Ibbi, babu wanda bai San Hamisu Bala Wadume ba. Har zuwa lokacin da aka kama shi, babu wanda zai iya gaya maka sana’arsa. Amma yana raba wa mutane hayar motoci na Sharon. Yana bada hayar Babura da kyautarsu Yana harkar mai. Yana raba wa mutane kudi a yi ta facaka da su.
Shi Hamisu Bala Wadume abokin ‘yan sanda ne. Abokin sojoji ne. Mutumin fada ne saboda yana baiwa kowa kudi ba kididdiga. Matasa da ‘yan mata suna rububinsa.
Wani Bayarbe mai safarar bindigogi ta haramtacciyar hanya mai suna Ojomo Adebowale Gbenga, ya ce ya yi kamar shekara shida da sanin Wadume, kuma alakarsu Wadume ya taba sayen bindigogi kirar AK47 har sau shida a gurinsa.
Asirin Wadume ya tonu ne a lokacin da suka yi garkuwa da wani attajiri mai harkar man fetur wanda sai da suka karbi zunzurutun kudi har naira miliyan 120 a hannun ‘yan uwansa. Ashe ‘yan sanda na IRT suna ta fakonsa. Tarkonsu ya kama shi a wuya ranar 6 ga Agusta 2019.Yau sati biyu Cif.
Yan sanda sun je kama Wadume a Ibbi, sun yi sa’ar kama shi suka sanya masa ankwa, Amma sai matasa wadanda suke cin kudinsa suka tada bore a wani guri Gindin Waya kusa da titin Ibbi zuwa Wukari. Kafin su kamo shi sai da suka je gurin yan sanda a Wukari suka fada musu mai ke tafe da su. Haka kuma sun ci karo da shinge biyu na sojoji.
Wadannan matasa sune suka biyo motar yan sanda dake .dauke da Wadume kuma su suka gaya musu ga wasu barayi sun zo sun yi garkuwa da shi. Tunda sun saba da shi nan take suka kai masa dauki. A shingen sojoji na farko ne, sojoji na shinge na biyu suka samu labari suka kai dauki. Da shingen farko dana biyu duk Kyaftin na soja Usman shi ya bada umarnin a yi harbi. An ce daga 9 ga watan Yuli 2019 zuwa 6 GA Agusta 2019 Wadume sun yi waya da junansu sau 191.
Da karfin bindiga sojoji suka kashe ‘yan sanda uku da civilian guda biyu. Daga cikin civilian har da wani mai suna Jibrin wanda yan sanda suka yi amfani da shi don kama Wadume. Yana cikin wadanda yaran Wadume suka taba kashe masa dan uwa.
Akan idon wani dan sanda sojoji suka harbe dan sanda bayan ya gaya musu shi jami’i ne, suka ce karya ne. Da suka gama kisan suka zaro ID card na mamatan yan sanda sai suka ce na bogi ne. Haka suka cire wa Wadume ankwa daga hannunsa suka ce ya yi tafiyarsa, suka gudu da shi a motar dake bin ta yan sanda, suka haura da shi kogin Ibbi zuwa Jos. A gaban jama’a matasa suka rika murna sun kwato Wadume da taimakon soja.
Daga baya sai ta bayyanarwa soja sun yi ganganci da su da yan sandan Wukari.DCO na yan sanda ya yi kokarin boye bayani amma ina, yanzu dai da kyaftin da wasu sojoji biyar da wasu yan sanda a Wukari da jama’a da yawa an cafke suna tsare, aka sake shiga laluben Wadume.
An kafa kwamitin bincike akan wannan dambarwa fuska biyu ta soja da kuma yan sanda. Cikin ikon Allah, yan sanda sun yi nasara a karo na biyu sun sake kamo Hamisu Bala Wadume. Sun kama shi a Hotoro ta karamar Hukumar Nassarawa a jihar Kano. Shi da kansa ya yi bayani cewa soji ne suka kwato shi, kuma su suka kwance masa ankwa, sannan kuma suka ce ya yi tafiyarsa..
Wannan lamari sai an bi shi a hankali. Sannan sai an bi shi an gano bakin zaren. Na gode wa Allah kuma na jinjinawa yan sanda. Wannan abin a yaba wa ‘yan sanda ne. In suna son yin aiki ba abin da zai gagare su.
GA HOTON WADUME A KASA