AN KARRAMA MARIATU BALA USMAN

0

AN KARRAMA MARIATU BALA USMAN

Daga Taskar Labarai

Zuriyar limamin Kano Zaharadden sun karrama hajiya Mariyatu Bala Usman tsohuwar kwamishiniyar lafiya ta jihar Katsina.

Taron wanda a ka yi shi a yau asabar a dakin taron na tsohuwar gidan gwamnatin Katsina da aka sani da gidan Sa’idu Barda.

Wakilai da suka wakilci mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da kuma wadanda suka wakilci mahaifiyar mai martaba sarkin Kano mai babban daki duk suna a cikin wannan zuriya ta limamin Kano Zaharadden.

Daga nan Katsina duk manyan shugabannin zuriyar dake nan Katsina sun halarci taron cikin su harda shugaban zuriyar dake nan Katsina, Alhaji Aminu Abdullahi da Mustafa Muhammad Inuwa sakataren gwamnatin Katsina da minista harkokin jiragen sama Alhaji Hadi sirika.

Zuriyar Dakta Yusufu Bala Usman sun zo kwansu da kwarkwatansu, karkashin jagorancin Alhaji Attahiru Bala Usman.

Manyan-manyan ‘yan siyasa har da shugaban jam’iyyar APC ta jiha Alhaji Shittu S Shittu Maslaha da shugaban jam’iyyar APC shiyyar Funtua Alhaji Bala Abu Musawa da zabbabun ‘yan majalisar jiha dana tarayya daga Musawa duk sun halarta.

Taron ya fara da jawabai na irin gudummuwar da hajiya Mariatu ta kawo a zamanta na kwamishinar lafiya a jahar Katsina. Sannan aka bata kyaututtuka na Alqur’ani mai tsarki da sallayar sallah da matallabin karatun Alqur’ani da zanen sunayen Allah mai tsarki don kafawa a daki.

Daga nan aka ci abinci, wanda kowa duk dakin taron sai da yaci abinci da nama da kifi da kaji aka barshi. An Kira hajiya Mariya don tayi jawabin godiya, wanda ta kasa don dadi da murna sai ta fashe da kuka ta ajiye abin maganar ta dawo kusa da mijinta Alhaji Mannir Abukur ta zauna.

Daga karshe Alhaji Attahiru Bala Usman shi ne yayi jawabin godiya a madadin Mariatu Bala Usman da sauran ‘yan gidansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here