MATASA DA SANA’ARSU

0

MATASA DA SANA’ARSU

Amina Waziri
~~~Taimakon Gajiyayye Tsanin Nasarar Rayuwa

Tare da Abdulrahman Aliyu

Kamar ko wane mako a wannan makon ma Taskar matasa da sana’arsu ta taskace maku bayanai kan Malam Amina Waziri mawakiya kuma fitacciyar ‘Yar gwagwarmaya mai fafutuka kan abin da ya shafi hakokin mata da taimakin gajiyayyu. Mun tattauna da ita kan a in da ya shafi rayuwarta da kuma wasu abubuwa masu kayatarwa, kamar yadda zaku ji data bakinta.

“Sunana Amina Umar Waziri, wacce aka fi sani da Amina Waziri Kaduna. Ni haifaffiyar garin Kaduna ce, mahaifiya ta daga Benue State, mahaifina daga Kano State, na fara karatu daga nursery zuwa primary a Abubakar Gumi College (Chanchangi). Nayi secondary daga JSS zuwa SSS a Tafawa Balewa Kabala Costain Kaduna. Na kammala a shekara ta 2008, nayi Saukar Alqur’ani a 2005, a nan na tsaya, ban samu na cigaba ba saboda wasu dalilai.

A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah, kwasam sai na tsinci kai na wajen koyan sana’o i na hannu daban-daban (kamar su: Dinki, dafe -dafen Abinci kala-kala, Man Shafawa, Sabulu na Ruwa, Turare, Tamba, waka da sauransu).

Bayan nan sai na yanke shawaran koma wa Makaranta, na sanar da mahaifiyata tayi farin ciki kuma tasa albarka, naje na cike form na jamb a shekara ta 2012, na rubuta ban samu ba, a shekara ta 2013 nayi register na Computer School a Skilled Aquisation under Word Processor for 9 month, nayi Industral Training (IT) a Kaduna State House of Assembly.

Kafin in kammala na kara cike Form din Diploma in Public Administration a A. B. U Zaria, na gama a 2015, a yanzu haka na koma Makaranta dan kammala karatu na, sannan kuma ina harkan kungiyoyin da dama na tallafama marayu, gajiyayyu da marasa galihu, kuma na cigaba da sana’o’ina dan dogaro da kai na”.

A bangaren waka kuwa Amina Waziri ta yi mana karin haske kan lokacin da ta tsunduma cikin harkar waka ka’in da na’in

“Na fara wannan Sana’ar a karshen shekarar 2012, hakan ya faru ne saboda sha’awa da shakku a kan Sana’ar da nake yi. Nasa mu riba da dama a fannin waka ta inda ban taba tunanin zan samu”

Amina Waziri ta bayyana mana cewa rayuwarta come take da riba da nasarori a dalilan sana’arta da ayyukan da tasa gaba na taimakon gajiyayyu da marasa karfi, in da ta yi mana fashin baki kamar haka:

“Cigaba da karatu na ya daya daga cikin riba da nasa mu a rayuwa. Daukaka, Baiwa, Sa’a da nasara duk suna cikin nasarori na rayuwa, shi yasa ako da yaushe nake godiya ga Allah (S W A) da irin nasarar da ya bani. Domin a kullum cikin farin ciki nake tare da jin dadin da baya misaltuwa, saboda ko haka Allah ya bar ni na samu ‘yancin kai na, ma’ana na zama independent woman ba dependent woman ba. Wani abun sai dai a ga nayi bana jiran kowa ya mun.

Sana’a sa’a ce kuma tana riba musammamma idan ya kasance zuciya da daya kuma tsakanin ka da Allah ka ke yinta, zaka samu cigaba da nasarori akan ta sosai idan ya kasance da albarkacin iyaye akan ta”

Da aka tambayeta game da shawarar da zata baiwa matasa ganin sun dogara da kansu sai fara da cewa,

“Shawarar da zan baiwa ‘yan uwa na maza da mata mu zamo masu kishin kammu ta fannin kama sa’a ko wacce iri har in dai bai saba wa addinimmu ba. Yanzu ba a zama waje daya, domun idan ka zauna waje daya zaka ga sakamakon yin hakan. Sana’a ko yaya take kada ka rainata, don ko watarana zata zamo abunda baka taba tunani ba a rayuwa.

Idan ka kasance kana da abun yi misali kamar sana’a irin tamu to ka huce wulakanci a wajen kowa. Sannan mu zama masu dogaro da kai da kuma taikmakon kammu da kammu, mu nema na kammu, mu tsare mutuncin kammu, mu cire kyashi da hassada a tsakanin mu, mu girmama na gaba da mu da na kasa damu, kuma mu kasance masu tallafawa na kasa damu dan ganin suma sun samu ‘yancin kansu.

Haka kuma ta yi mana Karin haske kan fitattun wakokin da ta yi wadanda suka fito da fadaharta da hikimarta a fili India ta bayyana cewa:

“Akwai wakar da nayi ma Tsohon Kakakin Majalissar dokoki na Kano wanda a yanzu ya koma Danmajalisar Wakilai wato Hon. Kabiru Alhassan Rurum. Akwai wakar Hon. Jabir Khamis, shugaban karamar hukumar Igabi, akwai wakar sarkin Hausawan Abuja , Akwai ta Sarkin Matasan Sokoto, da kuma fitattar wakar nan ta Khuci Khuci Hoteye Hausa Version da Duniya Labari da kuma Kalmar So. Da sauransu da dama

Amina Waziri dai na data daga cikin matasan da suka kawo sauyi ta fuskar dogaro da kai ga rayuwar matsa musamman mata, wadanda ke ganin ba cewa rigar da mace ya kamata ta sanya bata wuce biyu ta gidan iyaye da kuma ta gidan aure kawai, ba sai ta sanya rigar ilimi ba ko ta sana’a. Muna mata fatan alheri ga rayuwa, Allah ya kara daukaka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here