DARURUWAN MAGIDANTA A BIRNIN DAURA SUN RASA MUHALLANSU SAKAMAKON AMBALIYAR RUWAN SAMA
JaridarRijiyarKusugu 26-08-2019
Mun tabbata wadanda wannan abun ya afku gare su, sun yini kuma sun kwana cikin tashin hankali da bakin ciki sakamakon wannan masifa da ta afka masu. Da wannan muke mika kokenmu zuwa ga Sabuwar Ministar Humanitarian Affairs, Disaster Management, and Social Development, Hajiya Sadiya Umar Farouk, da kuma Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa (NEMA), Alhaji Mustapha Maihaja, da ku yi kokarin kai wa al’ummar mahaifar Shugaban kasa Muhammadu Buhari agajin gaggawa domin rage rad’adin masifar da al’umma suka shiga ciki sakamakon ambaliyar ruwan sama da ta afku a ranar Lahadi 25-08-2019.
Hakika, wannan shi ne lokacin da za ku nuna wa al’ummar mahaifar Shugaban kasa halasci daga ma’aikatarku. Allah ya sa wannan koke ya kai gare ku ??
Muna rokon Allah ya kare afkuwan haka a gaba.
#JaridarRijiyarKusugu 26-08-2019 ??