HAUSA BA DABO BA

0

HAUSA BA DABO BA

#RanarHausa

Wasu kalmomin Hausa masu ma’ana fiye da ɗaya.

1. RAMA
Rahamu ta taƙarƙare da cin ganyen RAMA kullum wai don ta yi maganin yunwar da ke sa RAMA, don ta ji an ce ramamme ba ya RAMA bugu.

2. KARA
Kallamu ya kora karsanarsa zuwa KARA domin ya sayar, a kan hanya ta ture wa Ali rumfar KARA da yakan kasa KARAn rake, da yake Ali mutum ne mai haƙuri da KARA sai ya yafe wa Kallamu.

3. KARE
Musa ya suri sandarsa da yake KARE da ita idan suna wasan karabkiya shi da Ja’e, ya nufi ‘yan dangullan da yake kiwo a guje domin ya KARE su daga wani baƙin KARE da ya hango yana dafafen su yana yaƙe haƙora.

4. ZUBA
Kande takan so ta ZUBA wa Habu miya da tantakwashi, idan miyar ta kai masa karo, ya fara ZUBA mata labarin da babu waƙafi balle aya, tamkar bishiyar da ganyenta ke ZUBA lokacin hunturu, takan dube shi ta bushe da dariya.

5. TAFI
Lokacin da Inde ya TAFI gidan Sarkin Noma domin ya roƙo TAFI uku na irin dawa sai ya jiyo matan gidan na daka suna TAFI da carabke.

6. RUGA
Audu ya RUGA da gudu yana dariyar ƙeta lokacin da ya wawushe sauran ɗanwaken da suke ci shi da Rabe ya RUGA shi duka a cikin baki, Rabe ya bi shi, suka yi ta guje-guje a cikin RUGA suka firgita zabi da kaji waɗanda suka haye saman damfami suna ta kwakwazo.

7. TUƘA
Kabiru ya TUƘA a-kori-kurarsa ya nufi siton Alhaji Audu Dankwangila domin ya ɗauko hatsin da za a TUƘA wa ‘yan makaranta tuwo, a kan hanya ya wuce Garba a cikin rumfarsa yana TUƘA (tubka) igiyar da zai ɗaure ragonsa da ya ci ya ƙoshi yana ta faman TUƘA abin da ya ci.

8. KURA
Wata KURA da ta kubce babu takunkumi a cikin ƙauyen Magangari ta sa wani mutum ya yi watsi da ruwan da ya turo a KURA, garin gudu ya ture wani yaro da ke janye da KURA (mayen ƙarfe) yana kama ƙananan ƙarafunan da ke turbuɗe a cikin ƙasa.

9. CAJI
Sule ya kai batirin wayarsa wajen mai CAJI, lokacin da ya CAJI aljihunsa domin biyan kuɗin sai ya ji babu ko ƙarfanfana, nan take ya juya da sauri domin ya CAJI Ɗari da laifin lalube masa aljihu lokacin da suke kallon ƙwallo.

10. TURMI
Mani ya saɓi TURMI guda na atamfa daga cikin shagonsa, ya nufi ƙauye domin ya kai wa Inna ziyara, lokacin da ya isa sai ya tarar da ita tana daka magani a TURMI wanda Buba zai shafa a mummuƙe saboda haƙoransa, TURMI, da ya yi kogo yana masa ciwo.

Ga kuma ƙarin wasu kalmomin, ko za a iya jaraba sanya kowace a cikin jimla tare da kawo dukkan ma’anoninta kamar yadda muka bayar da misali a sama? Kowa ya bar gida, gida ya bar shi. Bisimillah!

Rago
Gara
Dama
Zage
Mari
Waya
Gari
Sara
Gado
Fara
Fito
Guga
Gora
Baiwa
Kwaɗo
Rina
Sa’a
Dawa
Duma
Taki
Dare
Baƙi
Kuɗi
Wuri
Wari
Taro

(c) Bukar Mada
26/08/2019
Ranar Hausa Ta Duniya

#RanarHausaTaDuniya
#RanarHausa
#Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here