KARKAFBARAYI SUNYI WA GARIN WURMA KARKAF

0

KARKAFBARAYI SUNYI WA GARIN WURMA KARKAF
Daga taskar labarai
Barayin daji sun aukama garin wurma dake karamar hukumar kurfi ta jaha katsina sun masa karkaf sun kuma tafi da mutane sama da talatin a cikin daji..cikin su har da wani tsohon mataimakin shugaban karamar hukuma da wasu daga cikin iyalan mai garin.
Wani Wanda yaje garin na wurma don gano da yin jaje ga mutanen ya shaida wa wakilin taskar labarai cewa. An fada masa cewa barayin sun je garin tun karfe sha daya na dare har uku na dare suna a cikin garin suna barna.
Barayin sun kwance duk wata dabba sun tafi da ita, ba wani shago a garin da basu fasa ba suka debi abin da suke so.haka ma duk wani gida mai kyau sun shiga sunyi ta a sa.
Barayin sun tafi da mutane Ar ba in,daga baya suka sako mutane bakwai suka ce su dawo gida.daga cikin wadanda suka tafi biyu sun gudu daga hannun maharan.
Barayin sun so tafiya da maigarin, amma suka kyale shi bisa tausan cewa baya da lafiya kamar yadda suka shaida masa.amma sun tafi da wayar shi suka ce in ana bukatar magana dasu a Kira lambar mai garin.
Garin nan wurma ya zama kamar kufai, da akaje yau da safe.kowa na neman mafaka tsoron kada barayin su dawo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here