YAN BIYAFARA A GABAN OFISHIN JAKADANCIN NAJERIYA A KASAR JAPAN

0

YAN BIYAFARA A GABAN OFISHIN JAKADANCIN NAJERIYA A KASAR JAPAN
Daga jaridun taskar labarai


Wani hoton bidiyo da kungiyar nan ta inyamurai masu sun su balle da ake Kira IPOB wadda ke karkashin Nndi kanu suka saki a shafunkansu ba yanar gizo
.yanzu haka suna tsaye a jikin wani gida in da sukayi ikirarin nan ne ofishin jakadancin Najeriya. Kuma anan aka sauke shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A bidiyon anga yan sanda ke waye da gidan suna bashi kariya.kuma Kafin ka isa gidan sai an duba ka.
Mai magana a bidiyon yace su yan biyafara ne, da suka zo da niyyar sai sun gana da Aminu jibril daga Sudan Wanda ke ikirarin shine shugaban kasa Buhari a fadar su kamar yadda zaka ji suna nanatawa
A bidiyon an Nuno wadanda suke ikirarin yan biyafara suka ja daga yan sanda Japan kuma sukayi shinge a gaban wani gida da suka ce nan ne aka saukar da shugaban kasa.
Kungiyar IPOB ta saki bidiyon a duk shafukan sada zumunta da take amfani dasu wajen isar da sako ga duniya.kuma sun ce kai tsaye suke daukar hoton bidiyon suna watsawa
Taskar labarai ta tabbatar da ingancin bidiyon da kuma tabbacin yau aka dauki hoton. Amma babu tabbacin a wani bangare ne na kasar japan
Ana iya gani hotunan da kamar yadda muka dauko daga bidiyon da suka saki.
………………………………………………………………………
Jaridun taskar labarai da the links news.jaridu ne masu zaman kansu dake bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com da kuma thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta na yanar gizo

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here