SHARHIN TASKAR LABARAI; HABA KANTOMAN KURFI

0

SHARHIN TASKAR LABARAI; HABA KANTOMAN KURFI

Daga Jaridar Taskar Labarai

Mahara sun shiga garin Wurma dake karamar hukumar Kurfi jihar Katsina. Wani rahoto yace kafin su iso sai da suka rubuto takarda cewa suna nan zuwa don kawo Hari.

A ranar da zasu kai hari an ga maharan bisa babura kuma wadanda suka gansu sun yi tsammanin ko dai garin Wurma ko Tsaskiya zasu kaima hari.

Da barayin suka zo Wurma ba wani gida mai kyau da basu taba ba, duk wani shago sun balle shi sun zo cikin miyagun makamai.

Bayan sun gama ta’asa sun kuma kwashi mutane suka nufi dasu daji wata ruwayar tace mutane talatin wasu kuma sun ce sun fi hakan.

Lamari irin wannan idan ya faru wanda ya kamata ya fara kai dauki shi ne kantoman karamar hukuma, domin shi ne ke kusa da talakkawan kananan hukumomi.

Abin takaici wannan hari, da aka kaima wannan gari na Wurma, har sama da awa ashirin da hudu, amma sam baije jaje ba ko ganin me ya faru. Wanda wannan sam bai dace ba.

Mu a Taskar Labarai muna kira da wannan kantoma yayi nadamar abin da yayi kuma ya gyara daga wannan kuskure nashi.

A Taska muna jinjina ga Danmajalisar jiha mai wakiltar Kurfi da ya kwashe yini a garin Wurma don jajantawa mutanen sa.
………………………………………………………………………….
Jaridar Taskar Labarai jarida ce mai zaman kanta dake bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com tana da ‘yar uwa da ake bugawa da turanci mai suna The Links News dake a www.thelinksnews.com da kuma sauran shafukan sada zumunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here