YADDA MAHARA SUKA KAI HARI WURMA.

0

YADDA MAHARA SUKA KAI HARI WURMA.

Daga Taskar Labarai & The Links News

Ranar laraba 28/8/2019 wakilan jaridun Taska da The Links sun je garin Wurma karamar hukumar Kurfi ta jihar Katsina, domin jin ta bakin wadanda ibtila’in mahara ya shafa wadanda suka shiga garin daren litinin wayewar Talata.

Wakilan sun yi magana da maigarin Alhaji Mustafa Muhammad da kuma da yawa wadanda abin ya shafa.
An fada mana cewa maharan sun zo wasu a babura kuma wasu a kasa, sai da suka yi wa garin kofar raggo sannan suka harba wata bindiga mai kara harbi daya daga nan sai wasu bindigogi suka fara tashi da harbi.

Sun shiga garin da karfe 11.30 na dare, kuma sun bullo ta kowace kusurwa na garin, wani wanda ake jin kamar shi ne ogansu yana yawo yana ba sauran umurni yana cewa, “banda kisa banda kone-kone kudi kawai ko kayan kudi ko dabba”.

Basa fadin sunan kowa a cikin maharan kowa saje suke ce masa, zaka ji suna fadin kai saje yi kaza saje ga wasu nan saje, kowa saje ne a maharan.

Duk gidan da suka shiga magana daya ce, kudi ko wani abu mai daraja ko dabba ko abin hawa, duk inda basu samu dayan wannan ba to sai suce ma wanda suka samu ya biyo su daji an kawo kudi a amso shi.

Wani da muka tattauna da shi ya shaida mana yadda wadanda suka kama shi suka fada masa kodai ka bamu kudi ko mu tafi dakai daji, an kawo kudin amsar ka.

Duk maza a garin masu iya gudu neman mafaka sukayi a garin shi yasa mafi yawan wadanda aka tafi dasu daji mata ne, da yara kanana.

Maharan sun shigo da wadanda suka san garin da mutanen garin don an rika jin in zasu shiga gida zasu ce, nan gidan wane ne, za a samu kaza a gidan, ko kuma in sun kama mutum su sanya shi a gaba suce kaimu gidan wane.

Duk wani babur da dabba a garin sun kwashe, haka kuma duk wani gida da ke da wani abu sun shiga. Ba Wanda zai ce ga yawansu saboda dare kuma ga firgici amma an kiyasta yawansu da sama dari, don Wurma gari ne, mai girma a yankin.

Girmansa da tasirin sa a siyasa, ya Ssanya sau biyu ana basu mataimakin shugaban karamar hukuma a Kurfi. Garin yana da masu ilmi zamani sosai, an fada mana a yanzu haka garin na da sama da matasa talatin da suka gama digrin farko.

Maharan sun rika duba agogo. Can suka yi wata alama ta harbin bindiga sai barayin suka tattaru waje daya suka fara barin garin ta hanya daya.

Ganau ya fada mana cewa, yana bisa itace yaga an kora dabbobi da mutane kamar yadda ake Kamo bayi aka fita dasu garin. Kowane barawo da abin da ya sato a hannunsa da kuma makami rataye,suna tafiya suna shewa suna fadin saje yau tafiya tayi sa a.

Da farko sun tafi da mutane 49, wasu suka sulale masu suka sako wadansu wanda yawansu takai mutane 11, sauran wadanda suka rage a wajensu 38.

Sun tafi da wayar maigarin sukace duk wata magana ayi dasu da wayar, a gaban mu aka kira lambar barayin suka dauka har suka ba matan dake hannunsu akayi magana dasu.

Mun yi magana da matan suka ce mana an raba su biyar-biyar, kuma ana basu abinci ba cutar dasu ko muzanta su.
Mutum daya barayin suka sara da adda, wanda har suka ji masa ciwo, ana jin shi kadai ne wanda jin ciwo ya sama a harin na Wurma.

A ranar laraba kantoman karamar hukumar Kurfi Alhaji Jabiru Tsauri yaje garin da tawaga mai karfi inda ya jajantawa mutanen garin, yaje fadar maigarin ya kuma je wasu gidajen.

Dan majalisar jiha mai wakiltar Kurfi shima yaje a ranar Talata washegarin faruwar lamarin, inda ya tausayawa mutanen garin ya kuma fadi sakon gwamnan Katsina na nuna damuwarsa.

Tun faruwar lamarin gwamnan na Katsina ke ta taro da jami’an tsaro akan halin da jihar ta Katsina ke a ciki da wannan matsalar data aukama Wurma.

MUNA NAN TAFE DA WASU LABARAN DA SUKA SHAFI HARIN NA WURMA.
……………………………………………………………………
Jaridun Taska da The Links jaridu ne, masu zaman kansu dake bisa yanar gizo da sauran shafukan sada zumunta na yanar gizo suna a bisa shafi na www.taskarlabarai.com da www.thelinksnews.com ko lambobin whazzap na 07043777779, 07088895277

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here