HAJJIN BANA; KATSINA 2019: ANA DAF DA KAMMALA JIGILAR ALHAZAN JIHAR KATSINA
Abdulrahman Aliyu
@Jouney To The Holy Haramai
Ya zuwa yanzu an gab da kammala jigilar Alhazan jihar Katsina daga Kasa mai tsarki zuwa gida. A daren jiya ne da misalin karfe 11:09 jirgi na hudu ya sauka filin saukar jirage na Umaru Musa Yar’adu da ke Katsina dauke da alhazai kimanin 520 ‘yan asalin jihar Katsina.
Wannan jirgi dai shi ne na hudu, Jaridar Taskar Labarai ta zanta da wash alhazan a filin jirgin inda suka bayyana jin dadin su na sauke farali da suka yi da kuma dawowa lafiya cikin danginsu. Sun yabawa hukumar alhazan kan hidindimum da suka rika yi da su tun daga lokacin tafiyarsu har dawowarsu.
Kuma sun tabbatar wa Jaridar cewa kullum suna dukufa yiwa jihar su dama kasa baki daya addu’a samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Jaridar ta Tambayesu kan ko sun fuskanci wasu matsaloli? Mafi yawan Alhazan da ka zanta da su sun bayyana cewa ai ba a tuna baya, tunda dai Allah ya maido su lafiya kome ya wuce.