KARAMAR HUKUMAR RIMI: AN DADE ANA RUWA KASA NA SHANYE WA
Karamar hukumar Rimi tana ta dunbin tarihi na siyasa a jihar Katsina, haka kuma tana da zakararrun ‘yan kasuwa da malamai tare da gwarazan matasa masu kishin neman na kansu kodayaushe.
A yau 31/08/2019 shugaban riko na karamar hukumar Hon. Abdullahi Aliyu Turaji ya jagoranci shirya wani taro na karabar rahoton kwamitocin da ya nada domin su taya shi gudanar da ayyuka da kuma laluba masa matsalolin da karamar hukumar ke fuskanta domin magance matsalolin. Kwamitocin sun hada da bangaren ilimi da tsaro da lafiya da kuma na kudaden shiga.
Kamar yadda shugaban rikon ya bayyana, ya fadi cewa a lokacin da ya karbi jagorancin wannan karamar hukumar ya samu wadannan bangarorin cikin halin ni ‘ya su, wanda hakan ne ya sanya shi kafa wadannan kwamitoci domin gano matsalolin da suka haddasa faruwar haka da kuma hanyoyin magance su.
A wajen wannan taro da ya gudana a dakin taro na Muhammadu Sanusi II da ke jami’ar Al-qalam Katsina shugabannin kwamitocin dukkaninsu sun mika rahotonsu ga shugaban karamar hukumar tare da yin tsokaci kan abin da kwamitin nasu ya gano, haka kuma mahalarta taron sun yi bayanai da shawarwari na yadda suke ganin karamar hukumar Rimi zata samu cigaba, suma ‘yan siyasar da suka hakarci taron sun yi farfagandarsu wadda suka saba na fadar cigaba a baki kawai da kuma shafa wa mutane mai a baki ba tare da sun basu abincin sun ci ba. Koma da ya ke nan suma sun armasa taron.
Nasarori
Ko shakka babu a iya cewa an cimma nasara musamman wajen amsar rahoton dake dauke da wasu matsaloli da suke ciwa karamar hukumar tuwo a kwarya, a matsayin shugaban karamar hukumar da bai wuce shekara guda ba a karagar mulki ya yi iyakar yinsa na gano matsalolin da karamar hukuma take fuskanta ya kuma yi tunanin samar da wata gidauniya wadda ba ruwanta da siyasa domin a tallabi karamar hukuma, wannan babban abun a yaba ne matuka!
Matsaloli
Ko shakka babu wannan taron cike yake da kura-kurai, musamman ga wadanda suka shirya shi, kasantuwar shi shugaban karamar hukuma ya nesanta Kansa da shirya taron a cikin jawabinsa da ya gabatar a wajen taron inda ya bayyana cewa, shima gayyatarsa aka yi amma bai da hannu wajen shirya taron, su shuganannin kamitin ne ke da alhakin shirya wanna taro.
Matsala ta farko ga su wadanda suka shirya wanna taron ita ce, in dai har cigaban da suke kira da gaske ne to a karamar hukumar Rimi ya kamata a shirya wannan taro ba a Batagarwa ko Katsina ba, domin duo duniya irin wannan taro ana shirya shi ne a cibiyar inda matsalar take ba a tafi wani wuri ba, na farko za su rage kashe kudade musamman kasancewa dakin taron sai da suka biya, duk da dai ban da masaniya ko a kudinsu suka biya ba kudin karamar hukuma ba? wadanda kudin da aka kashe, kama daga dakin taro zuwa kwaliyyarsa za a iya samar da maganin da zai yi wata guda a MCH Abukur ko Tsagero ko Masobo ko Iyatawa, a nan an baranta da cigaba.
Wanda suka kira a matsayin babban mai jawabi a wajen Sam bai dace a dauko wani daga jihar Kano ba ace wai shi zai yi magana kan yadda za a inganta karamar hukumar Rimi, wannan sam kuskurene, wanda a cikin bayanan sa har ya ke ambatar Ajiwa a matsayin garin da ke cikin karamar hukumar Rimi, wanna gaskiya kuskure ne, shin duk karamar hukumar Rimi ba mai ilimin da zai yi wannan tun da magana ce, ake kan karamar hukumar Rimi?
Wani abun takaici ma ga makalar da aka gabatar ana magana fa ne kan yadda za a magance matsalolin dake addabar karamar hukumar Rimi ba wai matsalolin Nijeriya ba Baki daya kamar yadda shi mai gabatar da makala ya gabatar da makalarsa kan yadda kananan hukumomi yakamata su kasance da kuma nauye-nauyen da ke bisa kansu da yadda za su samu kudin Shiga da sauransu.
Ni na yi tsammanin za a dauko wani masani ne ya yi bincike wata kila kan matsalar fannin lafiya ko ilimi ko tsaro ko kuma sauran matsalolin karamar hukumar kamar rashin ingantattun hanyoyi da kauyukan karamar hukumar ke fuskanta ya jawo hankalin al’umma yadda za a magance matsalolin koda tsakanin al’ummar ne kafin gwamnati ta shigo ciki, misali rika kula da kayan gwamnati da kiyaye su, gudanar da ayyukan gayya kafin gwamnati ta shigo, shirya taruka na bita tsakanin al’umma domin wayar da kai.
Koyar da sana’o’i ga wasu dake cikin al’umma suke gudanarwa domin rage zaman banza, kai rahoton ganin wani abu na rashin aminta cikin al’umma domin magance matsalar tsaro da sauransu. Wadannan abubuwan na yi tunanin su makalar da aka gabatar ya kamata ta kalla, amma sai ta buge da sanar da mu abinda tsarin mulki ya tanatar wa kanana hukumomi, wanda hakan ya baranta ta da taron.
Duk da dai an kira taron na karbar bayanan da kwamitocin da aka samar suka gudanar, amma sai naga cewa a bangaren kwamitin samar da kudaden shiga ya kamata a gayyaci wasu masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Rimi kan kasuwanci da sana’o’in hannu irinsu Alhaji Salisu Continental ban Sani ba ko an gayyace shi bai samu damar zuwa ba ko turo wakili, irinsu mai Kamfanin Kadmash da saura Matadan ‘yan kasuwa da za a yi hadin guiwa dasu domin samar wa Rimi kudaden shiga da rage zaman banza.
Wata matsala da taron ya fuskanta shi ne kaucewa da’irar da aka shirya taron akai a kokarin ganin duk wani babban bako da yazo wurin sai an bashi dama ya yi magana.
Wata matsalar ita ce ta rashin gayyatar manyan eldoji a Rimi irinsu Mannir Abukur Kanal Remawa, Magaddai da Dagattai, wakilcin Kauran Katsina da kuma rashin girmama tsaffin ciyamomin da suka tallafi Rimi a baya iron su Maza Waje Hon. Nasiru Ala Iyatawa, Hon Gambo Abdulkadir da sauransu dai aka bar su can kujerar baya, duo da cewa suma sun gina Rimi ya kamata taron ya karamma su.
Shawara
Ni shawarata a nan daidai da wadda Maigirma Majidadin Katsina Hakimin Tsagero ya bada a wajen, in da ya bayyana cewa irin wannan taron an sha shirya shi a kashe kudade amma ba a aiwatar da abinda rahoton ya kawo, sai dai a zauna a sha lemu a tashi kawai. Ya yi kira ga shugaban karamar hukumar da kar wannan taron ya zama irin na shan lemu kawai an kashe kudade amma a gaza aiwatar da kome. Ya yi kira da a daure a aiwatar da abubuwan da kwamitocin suka samar.
In ba zan manta ba a shekarun baya lokacin da Kungiyar REDA na gudanar da ayyukanta taba shirya wani taro makamancin wannan wanda ta zagaya dukkan mazabun da ke Rimi ta wayar wa mutanen mazabun kai kan muhimmancin kungiya da kuma bayar da tallafi kan gidauniya, daga karshe aka hadu Rimi aka yi kwaryakwaryan taro na gidauniyar, amma kuma daga baya sai kungiya ta yi mutuwar kasa. A lokacin kowane dan karamar hukumar Rimi yana jin dadin kungiyar amma yanzu ta bata, kuma shugan REDA shi ne dai shugaban wannan kwamitin na yanzu, muna fatan kar shi ma wannan kwamiti ya yi irin mutuwar REDA. Allah ya Santa masu zimma irin wadda REDA ta yi a tashin farko.
Allah ya taimaki Karamar hukumar Rimi da mutanen ta baki daya.
Nagode
Abdurrahaman Aliyu