ALHAJI SALISU MAMMAN CONTINENTAL: BANGO ABIN JINGINAR TALAKAWA

0
552

ALHAJI SALISU MAMMAN CONTINENTAL: BANGO ABIN JINGINAR TALAKAWA

Daga Abdulrahman Aliyu

“Al’ummomin duniya kullum cikin shauki suke a lokacin da suke duba sabon jinjirin wata a sararin samaniya. Lokacin da watan zai bayyana zai taso ne a cikin tsakiyar taurari masu haske guda biyu zuwa sama a zagaye da shi. A ranar farko har zuwa kusan rana ta goma duk taurarin nan suna kawata hasken watan ne, amma daga rana ta sha biyu zuwa sama watan zai fito da tumbatsarsa ya shafe duk wani haske na miliyoyin taurarin da ke zagaye da shi”

  1. Na kawo wannan misali na sama ne domin kwatankwacin irin daraja da kima da wata ke samu a cikin tarin taurari haka Alhaji Salisu Mamman Continental ya samu shuhura da daukaka a cikin tarin mashahuran mutane da ‘yan kasuwa da ‘yan siyasa da ke karamar hukumar Rimi.

Alhaji Salisu Mamman Continental dan Bako ne da ya rikide ya koma rikakken dan kasuwa da al’umma ke amfana da shi ta matakai da dama. Ko shakka babu samun irin su Alhaji Salisu Continental a jiha ba karamin abun alfahari ba ne da tokabo, domin kaf din duniya irinsu masu zimmar taimako da kyautatawa Al’umma basu da yawa.

Kar na cika mai karatu da surutu bari na fara da ayyukan alheran da wannan bawan Allah ya shimfida a karamar hukumarsa kafin fitowa waje.

Ranar 11/08/2016 rana ce ta tarihi ba zai taba mantawa da ita ba a karamar hukumar Rimi, domin a ranar CE Alhaji Salisu Mamman ya mika makarantar da ya gina a mahaifarsa ta garin Kadandani, ita dai wannan makaranta rana da azuzuwa 12 da kuma ginannen dakin kwamfuta da kwamfutocin tare da ginanne ofishin shigaban makaranta da malamai, sannan kuma ya samar da malamai wadanda zai rika biya da kansa domin koyar da daliban makarantar. A iya cewa a tarihin jihar Katsina kaf babu wani mai kudi da ya taba gina irin wannan makarantar kuma ya mika ta kyauta ga al’umma ko shakka babu wannan abun alheri ne da tarihin duniya ba zai taba mantawa da shi ba.

Alhaji Salisu Mamman Continental ya gina tare da gyara rijiyoyin burtsatse a karamar hukumar Rimi wanda shi kansa ba zai iya fadar adadinsu ba.

Alhaji Salisu Mamman Continental ya tsunduma cikin harkar siyasa domin taimakawa gwamnati ta tallafi al’ummar shi da ayyukan raya kasa da gina al’umma. Hakan ya sanya ya dauki kudade ya bayar kowace mazaba dake karamar hukumar Rimi domin suyi ayyukan gina kasa da al’umma wadannan kudaden su aka yi amfani da su a wasu mazabun aka gina kwalbatoci da gyara hanyoyin karkara da samar da wasu abubuwa na more rayuwa.

Alhaji Salisu Mamman Continental ya dauki nauyin shirya tarukan bita ga matasa masu amfani da kafafen sadarwa a jihar Katsina Inda aka shirya masu taron bita kuma aka basu wayoyin hannu kyauta domin su mori amfani da zamani yadda ya kamata, matasa da yawa sun amfana da wannan shiri nasa.

A bangaren Kamfaninsa kuwa ya zuwa yanzu Alhaji Salisu Mamman Continental akwai ma’aikata sama da 100 dake aiki a karakashin kamfaninsa, wanda hakan ba karamin taimako bane da kishin ganin al’umma ta cigaba.

A cikin watan azumin da ya gabata ne Alhaji Salisu Mamman Continental ya yi wani hobbasa wanda ko gwamanti ta yi haka sai a yi mata sam barka Inda ya rarraba wasu kayayyaki da kudade domin al’ummar karamar hukumar Rimi suyi hidimar Sallah cikin jin dadi da kwanciyar hanakali, wadanda suka amfana da wadannan kayayyaki sun hada da:

(1) Masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Rimi (N500,000)

(2) Shugabannin jam’iyyar APC na karamar hukumar Rimi tun daga matakin mazaba wards zuwa karamar hukuma (N1,100,000)

(3) Ya bada atamfa guda (306) a raba ma mata na cikin karamar hukumar mazaba (wards) goma.

(4) Membobin kungiyar Manyan ma’aikata yan asalin karamar hukumar Rimi kowa atamfa guda (20) da (N100,00)

(5) Masu Makarantun Allo na cikin karamar hukumar (N350,000) su sayi naman sallah.

(6) Kungiyar Matasa masu hawan sallah na karamar hukumar Rimi (N50,000)

(7) Malaman makarantar Firamare da masu shugabantar kwamitin sakandire na garin Kandandani Da santar kiwon lafiya ta garin Kadandani da cibiyar jami’an tsaro ta yan sanda dake garin Kadandani (N100,000)

(8) Ya Bada tallafin miliyan daya don gina dakin gwaje-gwaje a makarantar Al’umma, dake garin Kadandani.

(9) Ya Bada kyautar kekunan hawa guda goma ga daliban makarantar sakandiren Al’umma dake Kadandani da suka fi hazaka.

(10) Ya bada Sa namijin saniya guda daya ga ma’aikantan shi bangaren na’ura mai kwakwalwa da sauransu, don su yi miyar sallah.

(11) Ya bada Sa Namijin Saniya guda daya ga ma’aikatan shi bangaren saye da sayarwa da motsa jiki GYM. Suma don suyi miyar sallah.

(12) Yaba Malamai Dattawa na Garin Kadandani (N100,000) su sayi naman sallah

(13) Komitin Darikar Tijjaniyya na unguwar Gabasawa Kwado ya basu gudumuwar (N100,000) don gina Islamiyya.

(14) Kungiyar Izala Islamiyya Jos dake unguwar Makera kusada Airport ya basu gudumuwar (N100,000) don gyaran masallaci da Islamiyya .

(15) Yaba kungiyar yan jarida reshen jihar Katsina da suka buga littafi na ayyukan gwamnatin APC a jihar Katsina daga 2015 zuwa 2019. (N250,000) da sauran abubuwan alheri da yawa.

Wani babban abun cigaba shi ne yadda Alhaji Salisu Mamman Continental ya sha alawashin gina gidan Talabijin da Rediyo domin bunkasuwar sadarwa a jihar Katsina, musamman duba da yadda muke da karancin irin wadannan abubuwa.

A wannan lokaci da muke ciki Alhaji Salisu Mamman Continental shi ne Elder na jam’iyyar APC a karamar hukumar Rimi, wanda a fagen siyasa ya taka muhimmiyar rawa da ta kawo wa jam’iyyar nasara a karamar hukumar ta Rimi.

Wasu ayyukan alheri da yake gabatarwa sun hada da bayar da tallafi domin karatu da kuma bayar da mota da wayoyi tare da kwamfutoci ga kungiyoyin da ke wa gwamnati hidima wajen yada ayyukan alherinta. Ko a cikin satin nan ya bayar da mota da kwamfitu da kudin kama ofis ga kungiya Masari Media and Enlightenment Forum.

Alhaji Salisu Mamman Continental ya kasance wanda kofarsa ke bude domin bayar da shawara ga matasa kan yadda zasu dogara da kansu.

A wannan iskan mai kadawa ko shakka babu akwai bukatar gwamnatin Rt. Hon Aminu Bello Masari ta rike shi hannun biyu-biyu musamman saboda kare martaba gwamnatin da taimakon al’umma da yasa gaba a koda yaushe.

Jaridar Taskar Labarai na fatan alheri ga Alhaji Salisu Mamman Continental.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here