AN GABATAR DA ADDU’AR SAMUN ZAMAN LAFIYA A JIHAR KATSINA
A yau ne al’ummar Musulmi suka taru a masallacin juma’a na Dahiru Mangal Inda aka gudanar da addu’o’in samun zaman lafiya a jihar Katsina.
Taron addu’ar ya samu halartar malamai da dama daga ciki da wajen jihar, tare da manyan jami’an gamnati.
A jawabin a mai girma gwamnan jihar Katsina Rt. Hon Aminu Bello Masari wanda ya samu wakilicin babban jojin jihar Katsina Musa Danladi Abubakar, ya bayyana cewa, “hakika Allah ya jarabci jihar Katsina da musiba amma cikin ikon Allah a bisa wannan addua’ da aka gudanar Allah zai karba mana ya kawo mamu sauki, ina son ku sani mai girma Gwamnan jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari yanzu haka tun jiya baya gari yana yankin Funtua wajen masu wannan barna domin neman sasanci dasu, saboda a shawo kan wannan matsalar.”
Malamai sun yi jawabi da dama in da suka jawo hankalin shuwagabanin da suji tsoron Allah a cikin Sshugabancin su, inda suka ce ku sani duk abinda ya faru ga al’ummar sai Allah ya tambaye ku daki-daki, dan haka kuji tsoron Allah ku tabbatar sun kare rayukan al’umma da dukiyar su.
Daga cikin malaman da sukayi bayani da kuma addu’ar gasu kamar haka: da Shiek Malam Abu Ummar, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Sarki, Malam Ibrahim Sabi’u Jibia, Shiek Liman Abbati Limamin Masallacin Juma’a na Alh Dahiru Barau Mangal, Shiek Malam Mukhtar Jibia, Shiek Abubakar Charanci, Malam Aliyu Baba, Malam Usman Namadi, Shiek Badamasi Abas, Malam Zakariya Alkashinawi, Malam Bilyaminu. Da sauransu da dama.
Allah SWT ya karba mana addu’o’in da aka gudanar ya dawwamar da zaman lafiya a jiharmu da kasa baki daya.