KWAMANDOJIN DAJI DA MASARI ZAI HADU DASU A BATSARI DA JIBIA

0

KWAMANDOJIN DAJI DA MASARI ZAI HADU DASU A BATSARI DA JIBIA

Daga Taskar Labarai

Ranar litinin 9/9/ 2019 gwamnan Katsina zai je yankin Batsari da Jibiya a rangadin da yake na ganawa da Fulanin daji masu dauke da makamai suna kai hare-hare ga Al’ummar yankin.

Taskar labarai ta gano su waye manyan kwamandojin wadanda dake rike da wannnan yankin kuma sune idan suka amince da zaman lafiya yankin ya samu sa’ida ke nan. Taskar Labarai ta gano da yawan mayakan da suke a karkashin su daga cikin su akwai wanda ake kira da Dangote Bazamfare dan asalin garin Dumburan ta jihar Zamfara. Ya dade a daji yana da mayaka sama da dari biyar karkashin sa, yana da muggan makamai. Yana da kamfacecen yanki da yake karkashin sa, ance har gidan kasa yake dashi don kauce ma harin jiragen sama, mayakansa ke sa ido a wasu yan kunan Zamfara da Jibia.

Matashi ne wanda ya dara shekaru talatin bai kai arba’in ba ya shiga daji ne saboda wani zalunci da yake koken an masa, ya amince zai halarci zaman.

Sai kuma wani da ake kira Dankarami, yaro ne wanda bai kai shekaru talatin ba yana da mayaka sama da dubu da suke jiran umurnin sa, mahaifiyarsa daga yankin Batsari take, mahaifinshi daga yankin Zamfara hatsabibin gaske ne, wadanda suka san shi, sun ce bai yi kama da wanda zai iya daukar makami ba, siffar jikinsa ta sanya, yana iya sajewa da mutane ba tare da ka gane shi ba, shima an zauna dashi ya amince zai halarci zaman.

See also  FG completes 2,465 Housing units through NHP – Official

Sai Mai kome matashin dattijo ne, don ya kai shekaru arba’in a duniya ko sama da haka da kadan yana da mayaka masu yawa karkashinsa, shekarunsa ya sanya yana da hangen nesa da iya tsara lamari, kuma dabarsa ya na shimfida mulki ne kamar wani maigari. Shima ya amince zai halarci taron zaman sulhun.

Da Dankarami da Maikome kansu a hade yake, saboda asalinsu yaran Buharin Daji ne. bayan an kashe shi suka samu ‘yancin kansu, suna yakar Dangote wani lokaci.

Akwai Dogo Gide wanda yake yankin Safana amma yakan dan yi ratse ya shigo yankin Jibia da Batsari ya kai hari ya koma. Dogo Gide shi ne wanda ya kashe Buharin daji yanzu kuma yana nan cikin dajin Rugu da Kamuku yana watayawarsa.

Wani fitinanne maharin shi ne Dogo Idi, wanda lokacin tashen shi yayi rashin imani, har ana masa kirarin ko da tsiya ko tsiya tsiya, in yana neman abu wajen ka sai ya samu. Dogo Idi ya haukace yana rayuwa a dajin cikin mafi kaskancin yanayi.

Wadannan sune kashin bayan zaman lafiya daga hare-hare a yankin Batsari da Jibia, kuma duk sun amince zasu gana da gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari a gobe., in ya kai ziyara yankin.

Allah ya sanya zaman ya kawo karshen halin da ake ciki. Amin.
________________________________________________
Taskar Labarai da The Links News jaridu ne masu zaman kansu dake bisa yanar gizo a www.taskarlabarai.com da kuma www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta da na layin whatsapp 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here