MATASA DA SANA’ARSU: YUSUF SANI~~ DOGARO DA KAI MATAKIN NASARA
Tare da Abdurrahman Aliyu
Shirin matasa da sana’arsu na wannan makon ya lalubo maku wani shahararren matashi daga garin Gusau na jihar Zamfara, inda ya bayyana inda muka ji kadan daga cikin tarihin rayuwarsa da kuma irin gwagwarmayar da ya yi wajen tabbatar da nasarar rayuwarsa ta fiskar dogaro da kai. Farko ya bayyana mana kansa kamar haka:
Sunana Yusuf Sani, an haifeni a 8 December 1989 a cikin garin Gusau, Jihar Zamfara, nayi karatun firamare duk a Garin Gusau na jihar Zamfara.
Game da fara Sana’a kuma Yusuf Sani yayi mana karin haske kamar haka.
“Na fara sanaa shekara biyar 5 da kusan wata shidda kenan
Ina saida wayoyin hannu, kayak gyaran wayoyi da kuma gawayi (charcoal) a nan Bebeji plaza a unguwar sabon gari Gusau. Gaskiya alhamdulillahi ta sanadiyar wannan sana’ar nasa mu cigaba kamar haka: Na gina gida ga kuma karatuna da na cigaba sanna kuma ga shi nan ba da jimawa ba zan yi aure insha Allah, duk ta dalilin wannan Sana’a da na rika da hannu biyu-biyu”.
Game da kalubale da dalilan da yasa Yusuf ya tsunduma cikin wannan sana’a ya bayyana mana cewa, A da yana ganin kamar mai aikin gwannati yafi more rayuwa, amma ashe abun ba haka bane saboda, abin da dan kasuwa zai samu a wata yafi abun da wasu ma’aikata ke amsa a wata, kuma shi cikin kasuwanci babu zullumi kamar yadda ma’aikaci zai rika yi duk karshen wata.
Yusuf Sani ya yi kira ga matasa da su tashi su nemi sana’a komai kankantarta, tafi zaman banza ko da kuwa kana aiki yana da kyau ka kara da sana’a saboda shi ma da kadan yafara, kuma Allah ya albarkaci Sana’ar.
Ya kara da cewa ita sana’a komin kankantarta ba abin renawa bace, domin cike take da nasara da cigaba, kuma duk wani dan kasuwa da ya tumbatsa daga sana’a ya fara. Yana fatan matasa zasu rungumi sana’o’i domin dogaro da kansu da kuma tallafawa rayuwarsu wajen ganin kasarmu ta inganta ta kuma fita tsara.