IDO DA IDO DA FULANIN DAJI MASU MAKAMAI

0

IDO DA IDO DA FULANIN DAJI MASU MAKAMAI

Daga Danjuma Katsina

@Taskar labarai da The Links News

Ranar litinin 9 ga watan Satumba na kama hanyar zuwa Batsari daga Katsina don halartar taron da gwamnan Katsina zai yi da Fulanin daji masu rike da makamai wadanda suka addabi yankin da hare-hare, kisa da kwasar masu dukiya.

Tawagar gwamnatin Katsina sun tafi a manyan motoci da zugar Kwamba, ni nayi niyyar tafiya da motata don duk inda na bukaci tsayawa in tsaya inga dil in kuma yi magana da duk wanda na keso. Na kuma yi niyyar daukar wasu a yankin Batsari da suke aiko ma da Jaridun Taska da The Links rahotanni labaran abin dake faruwa a yankin.

A hanyar zuwa dajin da za ayi taron naga filin kasar noma mai kyau amma bana ba a iya noma ta ba saboda Fulani masu makamai sun hana, naga wasu wuraren da aka cisu da yaki, ga shukar ta fito amma noman ya gagara. Na ga filin da aka yi niyyar yin mazaunin soja amma aka fasa, naga makarantu da yanzu an bar makaranta saboda mahara zasu iya sace malaman. An fada mani maharan malaman asibiti kadai ke basu tabawa, saboda suna tambayarsu magunguna da shawara akan lafiya naga garuruwa da aka tada ba kowa sai tsaffi da marasa gata, naga bi hanyar mai kwazazzabai da ban taba ganin irinta ba naga babbar motar gwamna ta kafe naga wata hilux ma ta kafe balle kana nan motoci yan bura-bura, kusan duk motar da ta isa filin taron da suka kira filin tanki ta samu rauni a jikinta.

Daji ne tsakiya ihunka banza, ba ka iya samun waya ko wacce ce wajen an fada mani tsakiyar matattarar maboyar fulanin dajin ne, masu dauke da makamai.

See also  mawallafin jaridun katsina city news.

Na rika ganawa da fulanin nan a gefe, kusan duk wadanda nayi magana da su babu wanda bai san yadda ake saraffa bindiga ba, ba a yarda wani yazo da bindiga ba sai jami’in tsaro. Amma kashi casa’in da tara da digo daya na Fulanin da suka zo taro suna dauke da Adda ko wuka a sake da su.

Wasu sun boye bindigoginsu a can nesa da inda ake taron wani ya jani ya kai ni wani kwari ya buda mani wani tarin ciyawa naga wasu buhun nan garara, mutumin yace mani bindigogi ne aka boye koda yanayin zai canza.

Ban samu ganin kwamanda Dan Karami ko Dangote ba amma naga wakilan su har mun dade muna tattaunawa ta hira. A matsayina na Danjarida don samun bayanai da dumi-dumi kuma in gantattu har na karbi lambobinsu amma ban basu tawa ba.

Na dau hotuna da irin wadan nan Fulanin masu makamai da ma na taba daukar irin wannan hoto da Buharin daji a taron da aka tabayi da shi a garin kankara kafin a kashe shi.

Sun tabbatar mani cewa uwayen gidajen nasu basu nesa da daga filin taron kuma suna jin duk abin dake faruwa. Daya ya fada mani dalilai da kila suka hana su fitowa.

Naga kwamanda Maikome, amma kafin ya fito wakilan shi sun yi ma taron magana.

Naga manyan wasu masu dauke da makaman wasunsu naji dalilai da suka sanya su shiga daji, wasu dalilan na zaluntarsu da aka yi ne da kuma mai da su basu da wata mafitar da ta wuce wadda suka dauka.( zan ci gaba)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here