ME YA HANA KWAMANDOJIN DAJI ZUWA TARON BATSARI

0

ME YA HANA KWAMANDOJIN DAJI ZUWA TARON BATSARI

Daga Taskar labarai

Wakilan Taskar Labarai sun yi zuzzurfan binciken me ya hana manyan kwamandojin daji guda biyu halartar taron da aka yi a dajin Batsari?

Wasu na kusa da mutanen dajin sun fada ma wakilan mu cewa, rashin yadda da juna a tsakanin bangaren su Dangote wanda yake cikakken Bafillace ne da Dankarami wanda yake asalin sa babarbare ne, da Mai kome na daga cikin abinda ya haifar da wannan matsala.

Wani ya shaida ma Taska cewa, akwai bakar gaba a tsakanin Dangote da Dankarami, wanda ta taso tsawon shekaru kuma abin da ya haifar da ita yana da wahala a samu madafar gyara ta.

Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa duk manyan bangarorin guda uku sun tura zaratansu cikin shirin koda zata baci a tsakanin su.

Majiyar mu tace yankin da aka yi taron yanki ne da mutanen Dankarami da Maikome suke da karfin gaske, wannan ya sanya Dangote shima ya turo yaransa masu yawan gaske kuma cikin shirin kota ware kota waraye.

Majiyar mu tace kusan dukkaninsu suna a sake kusa da wajen suna ji da kuma saurarar me ke faruwa.
Wannan ya aanya gaf da tashi sai ga Maikome da wani na kusa dashi mai suna Buratan Daji. Sannan ana cikin taron wata majiya tace sakataren gwamnatin Katsina Dakta Mustafa inuwa yaje har inda Dangote yake a sake, ance sakataren gwamnatin yayi-yayi Dangote yazo taron kodan yaga gwamnan Katsina amma yaki yace shi kunya yake ji, an taba yarjejeniya dashi amma yaci amana.

Majiyar mu tace rashin haduwar wadannan kwamandojin uku wuri guda na iya zama Alheri don yana da wahala su hadu a tashi lafiya musamman tsakanin Dangote da Dankarami. Wanda ko dan tsakanin nan Dankarami yaje Ruggar Dangote ya kwashe masa dabbobi.

Majiyar mu ta tabbatar mana dukkanin su suna da bukatu daban-daban, amma sun fadi wasu basu bayyana wasu a wajen ba.

Daga cikin wadanda basu bayyana ba akwai yadda za a hana jirage yawan jefa masu bama-bamai daga sama wanda suke kashe masu mata da yara da kuma dabbobi da kuma kyale su su rika watayawa da makamansu amma a cikin daji da in zasu yi tafiya wani yankin a kyale su su tafi da makamansu kuma zasu rika haka ne don kariyar kansu daga abokan adawarsu, ba don wata manufa ba inji wata majiya daga cikinsu.

A wurin sun bada shawarar a sako masu mutanensu a kyale su su wataya su shiga duk inda suke so. Majiyar mu ta tabbatar manyan sun amince da zaman sulhu amma kila a dan dau lokaci ana fama da yan kananan barayin dake da makamai a hannunsu.
………………………………………………………………………..
Taskar Labarai Jarida ce mai zaman kanta dake bisa yana gizo na www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta tana kuma da ‘yar uwa ta Turanci mai suna The Links News dake a www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta. Layin kira ko whatsapp shi ne 07043777779, 07088895277

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here