SADIO MANE YA GINA MAKARANTA A KAUYENSU

0

SADIO MANE YA GINA MAKARANTA A KAUYENSU

Daga Ibrahim Hamisu

Dan wasan kwallon kafa ta Liverpool da ke Ingila, dan asalin kasar Senegal Sadio Mane ya gida babbar makaranta a kauyen Bambali da kudinta ya kai E270,000.
A baya bayan nan ma dai Dan wasan ya gina katafaren Asibiti, sannan ya ke daukar nauyin ganin wani filin wasa Stadium ga mutanen garinsu mai suna Seidio da ke kudancin Sanegal. Sannan ya rarrabawa marasa karfi kudi da yawansu ya kai 50,000 CFA duk wata.

A shekarar da ta gabata ne dai Mane ya baiwa dagacin kauyensu Miliyan 200 domin a gina Makaranta da Asibiti da kuma Masallaci sakamakon kauyensu babu wadatattun abubuwan da aka lissafo,

Mane mai shekara 27 ya zura kwallaye 22 a gasar Primiya da ta gabata wato 2018/2019, yayin da ya ci kwallaye 13 a gasar zakarun Turai Champion’s League,

A watan da ya gaba ta ne dai kasar Sadio mane Senegal ta buga wasan karshe da kasar Algeria a gasar zakarun nahiyar Afirka Nation Cup inda Algeria tai nasara da ci daya mai ban haushi inda ta daga kofin.

Mane dai ya zo Liverpool ne daga Southampton a shekarar 2016, A zamansa na Liverpool ya buga wasa sau 159, ya ci kwallaye guda 66 sannan ya taimaka aka ci kwallaye sau 22.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here