ABINDA YA SA MUKA DAU MAKAMI

0

ABINDA YA SA MUKA DAU MAKAMI

Daga Taskar Labarai & The Links News

Wakilan taskar labarai sun bi duk inda tawagar gwamnan Katsina ta taka don ganawa da mutanen daji a kowace karamar hukuma sun rika magana da masu dauke da makaman nan a gefe don ji me ya kaisu ga haka?

Kusan duk inda suka zanta da su dalilai biyu ne suke badawa wasu sun rika bada labarin yadda zaluncin da aka rika yi masu babu yankewa ya sa suka yanke hukuncin daukar matakin da suka dauka.

Wani a Faskari ya bamu labarin yadda aka kashe kanensa shakiki wajen azabtarwa, kuma aka nemi kama shi ya arce kuma ya fada daji.

A kankara wani ya bamu labarin yadda aka rika fasikanci da matarsa, da ta haihu kuma yaje ya nemi bin hakkin abin da aka yi masa mai maimakon ya samu hakkin sai kawai aka nemi ransa don haka ya balle ya shiga daji.

A Safana wani ya bayyana mana yadda aka tarwatsa shanunsa yaje ya gansu kuma ya nemi a bashi abinsa sai aka nemi ranshi don haka ya fada daji.

A Danmusa kazafi aka yi ma wani ya sai da komai da ya mallaka ya kwaci kansa da kyar da ya fito ba shanun kiwo ba wata sana’a dole ya dauki makami.

A Batsari gaban gwamnan Katsina wani ya bada labarin yadda aka kama shi, ya sai da komai ya zama kufai sannan ya fito, yace da ya fito gidansa ma bai gane shi ba.

Kusan labarin daya ne, yadda da yawa zalunci ya mai dasu daji, akwai kuma wasu da suke daukar makami don daukar fansa akan abin da wasu ‘yan uwansu fulani suke yi masu, wasu kuma don kare kansu da kansu daga farmakin jami’an tsaro ‘yan uwansu fulani da sauran mutanen gari.

Binciken mu ya tabbatar mana da makamai masu yawan gaske na hannun mutanen daji, wata babbar illa dake faruwa ita ce sukan sayi bindiga da sun saye ta abin farko shi ne dole awo aikin da zata mai da kudinta, don rike su ya zama riba.

Wata illar kuma matasan dajin nan da suka iya saraffa bindiga kuma aka bata su da kwayoyi da kashe kudin banza ga jahilci gaba da baya ga babu wani abin yi.

Bincike ya tabbatar da cewa rufe shafin wannan mummunan babi na bukatar tsari, amintattu masu gaskiya da kuma kudin da za a yi shiri na musamman na ilmantarwa da aiki ga mutanen daji yana kuma bukatar lokaci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here