0

*TARIHIN SHEIKH ABUBAKAR AL-MISKIN*

*NASABARSHI*
Shi ne Abubakar bn Ahmad bn Maidugu Kyara wajhi bn Muhammad Maina(yanbu Muhammad) bn Mai Ali bn Mai Hajj bn Mai Daunama bn Mai Ali bn Mai bn Umar Mai Idris Aloma bn Mai Ali bn Mai Idris Katagarma bn Mai Ali bn Mai Danoma bn Mai Beri bn Mai Idris bn Mai Ibrahim bn Mai Beri bn Mai Danoma bn Mai Hami bn Mai Jal bn Mai Shiyu bn Mai Arko bn Mai Bello bn Mai Biyoma bn Mai Kadhori bn Mai Arshu bn Mai Kani bn Mai Doka bn Mai Ibrahim bn Saif bn Zee Yazai bn Aslam bn Zaid bn Sahlu bn Amru bn Qais bn Mu’awiya bn Jism bn Abdu Shams bn Wa’il bn Awf bn Humair bn Kadn bn Awf bn Zahir bn Ayman bn Humair bn Saba’i bn Yushjab bn Yu’urab bn Qahdan bn Abar bn Ashalik bn Arfakashad bn Sam bn Nuhu(A.S) bn Laamik bn Mattushalak bn Aknuk bn Yarid bn Mahlailu bn Qainan bn Anush bn Shitu bn Adamu(A.S), shi kuma Adamu daga yumbu.

*HAIHUWARSA DA TASHINSA*
An haife Shaykh Abubakar Al-Miskin da alfijir din ranar lahadi, tara ga watan rabiul awwal, shekarar 1337 bayan hijrar Annabi Muhammadu Sallallahu Alayhi Wa Sallam a Hayin Hausari Zango Yarwa.
Ya taso a wannan Anguwar da neman ilimi tun ya na qanqani, yayin da ya kai kimanin shekaru biyar sai mahaifinshi ya turashi don yin haddar Al-qurani Mai Girma a wurin wani Mahaddaci kuma Gwani Mai Suna AJI KANAMBO. Abinka da na Allah, cikin shekaru bakwai da ‘yan watanni ya haddace Littafin Allah Mai Girma. Daga nan ya lazimchi malaminsa da aka ambata domin ya qara tabbatar da haddarsa bisa ga al’adar mutanen Borno, bayannan ya dawo wurin mahaifinsa domin ya karanchi sauran ilmai a wajansa.

*NEMAN ILIMINSA*
Da farko Shehu Al-Miskin yayi karatun ilimin Tauhidi, Fiqhu da Tafsirin izu biyar (5) a hannun mahaifinsa. Bayannan Mahaifinsa ya rasu yana da kimanin shekaru sha biyar (15). Sannan ya tafi zuwa wajen Mu’allim Sani Mahamai domin karatun Tauhadi da Hadisi. Yayi karatun ilimin Falaki a wajen Sayyid Isma’il Abdullahi.
Bayannan ya samu ilimin yanayi, ilimin hisabi, ilimin taurari da ilimin Nahawu da Aqaa’idu a hannun Mu’allim Bulama Kura.

*TAFIYOYIN QARIN ILIMI*
Shehu Al-Miskin ya bar garinsa ta haihuwa ya nutsa cikin duniya don neman qarin ilimi yana mai koyi da mahaifinshi da kuma magabata na farko.
Da farko dai ya sauka a wata Alqarya da ake kira Marwa a Jamhuriyar Kamaru (Cameroon) in da ya hadu da Mu’allim Bukar Garbu, ya zauna da shi na tsawon shekaru biyu ya karanci Adabin Larabci. Sannan ya hadu da Modibbo Yahaya a Kwase da Modibbo Buhari a Garwa. Daganan sai ya nufi qasar Chadi (Chad) ya hadu da shahararrun Malaman qasar kaman Alhaji Muhammadu Aminu wanda aka fi sani da Gwani Laminu, in da yayi karatun tauhidi da Ilimin Sufanci a gurin sa.
Sai Shehu Al-Miskin ya dosa qasar Nijar (Niger Republic) inda ya amfana da malamanta kaman Alhaji Adam Addamagari wanda ya karanci Sharhin Ibn Adda’i. Sannan yayi karatun Isdila’in Hadisi a hannun Shaykh Muhammadu Sharif wanda aka fi sani da Gwani Sharif.
Bayan Nijar sai ya nufi Qasar Misra inda yayi karatu a hannun Shahararren Malamin Hadisinnan Shaykh Muhammad Hafiz At-Tijani, sai ya ziyarci qasar Lebanon cikin babban birnin Beirut yayi Karatu a wajen Shehu Muhammadu Al-Hariri almajirin Imam Yusufun Nabahani.
Sai Shehu Al-Miskin ya juyo zuwa Qasar Maghrib (Morocco) don ya ziyarci Shaykh Nazifi (Sahib Yaqutatil Farida). Bayan ya isa sai ya tarar da yayi wafati amma ya sadu da Khalifansa inda yayi karatun ilimin Hisabi a wajensa.
Shehu Al-Miskin bai taqaita neman iliminsa ba ga iliman littafai ba, bari dai ya amsa ilmai a hannun masunta na daga ilimin dabbobin ruwa da ire-iren kifaye; da kuma masana daji na daga abin da ya shafi namun dawa da tsuntsaye da bishiyu.
Bayan kammala neman ilimansa, sai Shehu Al-Miskin ya komo mahaifarsa wato Maiduguri a tsakankanin 1360-1363 domin yada ilimi ta islamiyya da raya Al’adun musulunci na daga fannonin illimai da ya tattaro ta hanyoyin wallafe-wallafe da kakkafa Islamiyyu.

*HIDIMARSA GA QASA.*
Shehu Al-Miskin ya tallafa a hukumomi da dama domin daukaka zamantakewa da halin Al’umma a ofisoshi da dama kamar.
1. Alqali a Kotun Qoli ta Borno (High Court), 1957.
2. Member Islamic Council, Kaduna, 1950.
3. Overseer High Islamic Colleges, Borno, 1977.
4. Amirul Hajj a Chadi (Chad), 1978.
5. Shugaban kula da mahajjata a Borno, 1979.
6. Shugaban kula da Kulliya ta Sharia da Islamiyyu a Borno, 1989 da sauransu.

*MATAFIYARSA A SUFANCI*
Shehu Al-Miskin dan Dariqar Tijjaniyya ne wacce ita ce dariqa mafi girma a Africa ta yamma. Ya amsa Dariqa a hannun mahaifinshi, Shi kuma mahaifinshi na daga cikin wadanda suka karbi Dariqa a hannun Shehu Ummaru Futi a yayin da ya ziyarci daular Barno a Shekarar 1266 AH. Shehu Al-Miskin yayi tarbiyya a hannun Shaykh Ahmad Abul-Fathi.

IJAZOZINSA
Haqiqa Shehu Al-Miskin ya samu ijazozi da dama na ilimi wanda a iyakance za su kai kimanin 2600. Ga kadan daga cikinsu kamar haka:
1. Ijaza a Dariqar Tijjaniyya daga Shaykh Muhammadul Hadi Mawlud Faal, 1370.
2. Ijaza a Dariqar Tijjaniyya daga Shaykh Adam Addamagari, 1380.
3. Ijaza a Ilimi da Dariqar Tijjaniyya daga Shaykh Ibn Umar bin Shaykh Muhammadul Kabir, 1380.
4. Ijaza a Ilimi da Dariqa daga Shaykh Muhammadu Kabir Khalil, 1383.
5. Ijaza a Ilimi da Dariqa daga Shaykh Ibrahim Inyass Al-Khaulakhy, 1387.
6. Ijaza na koyar da karatun Al-Qur’ani ta Isnadin Imam Nafi’u daga Shaykh Ibrahim Inyass Al-Khaulakhy, 1388.
7. Ijaza na karatun Al-Qur’ani da karantar da shi daga Shaykh Abubakar Atiku, 1389.
8. Ijaza a Ilimi daga Shaykh Imam Ali Cisse, 1387.
9. Ijaza daga Shaykh Muhammdu Gibrima,1361 inda ya ce:
“يا أخي تقدمتك في السن وأخذتك قبلك الإجازات عن الشيوخ ولذلك قدمتك لا اني أعلم منك ولا أفهم وإنما الإجازات والإسناد طريق المحدثين وسنتهم فبها يعرف ما ضعف من الحديث وما صح منها”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here