_WANE LITTAFI NE MAI SUNA YAR TSANA ?

0

_WANE LITTAFI NE MAI SUNA YAR TSANA ?
Daga barista Abdu bulama bakarti

‘Yartsana na Ibrahim Sheme na ‘daya daga cikin litattafan da na saya zuwan da na yi Najeriya kusa da Sallar Layyar da ta gabata.

Ha’ka’ki marubucin ya yi 6arin basira da hikima. Ya yi zuzzurfan bincike a kan karuwanci kuma ya yi bala’in iya ‘kagawa da tsara labari. Ga shi kuma ya masifar fahimci al adar Mallam Bahaushe ya kuma kwarance wajen karin magana da wa’ko’kin gargajiya. Lalle, Ibrahim Sheme ya cancanci yabo.

Amma karshen littafin bay yi mini da’di ba. Sam bai kamata a ce Zainab (wato Asabe) ta mutu ba. Dacewa ya yi a ce ta yi matuqar shan wahala amma daga karshe ta cimma burin na auren Tijjani Ahmed, wanda dalilin sa ta bar garin su, ta kuma tsinci kan ta a harkar kilakanci.

Maimakon haka, sai ta mutu, mutuwar wulakanci kuma ba tare ta yi wata cikakkiyar tuba ba. A d’aya bangaren kuma Bebi Sai-Tumoro wadda ita ta bada gudumowa wajen gogar da Zainab a hakar tsageranci ta tuba kuma ta aure Tijjanin Zainab. Ka ga kenan abin ya zama “kura da shan bugu ‘kato da kwashe kudi”.

Haka kuma ba abinda ya sami Alhaji Maidogonsoro wanda tun farko shi ya yaudari Zainab. Ya yi mata ciki kuma ya yi dalilin barin ta garin Naggetu.

Amma duk da haka, wannan labari ya yi matuqar ma’ana. Fadakarwa ne ga iyaye masu yi wa ‘ya’yansu auren dole saboda son zuciya. Wa’azi ne ga ‘yan mata ma masu azar6a6in barin gidan iyayen su dalilin saurayin da shi ba zai bar gidan nasa iyayen dan su ba. Darasi ne ga dukkan al-umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here