BAYAN SULHU; SU WA SUKA KAI HARI A BATSARI?

0

BAYAN SULHU; SU WA SUKA KAI HARI A BATSARI?

Daga Taskar Labarai

Taskar Labarai tayi zuzzurfan binciken akan suwa su ka kai hari a garin Batsari jihar Katsina, duk da cewa gwamnan Katsina yayi ganawar sulhu da manyan kwamandojin dajin dake yankin?

Wakilan mu sun yi magana da hadda wasu majiyoyo dake cikin dajin kuma daga duk ɓangarorin manyan kwamandojin guda uku waɗanda suka tabbatar mana da cewa ba mutanensu bane.

Sun faɗa mana cewa harin wani ne, ya jagorance shi wanda yake ganin kamar ba a ɗauke shi da muhammaci ba a taron sulhuntawar.

Majiyarmu tace, suna da masaniyar yana shirin kai hari nuna fushi kuma suka shaida wa wasu da suke magana dasu a ƙaramar hukumar cewa, akwai yiyuwar wani ya kai hari.

Duk manyan kwamandojin sun rungumi wannan sulhu wanda har ranar litinin da ta gabata 16/9/2019 an yi taron majalisar tsaro ta karamar hukumar Batsari kuma duk wakilan Fulanin daji masu ɗauke da makamai sun halarta, har suka bada haƙurin akan harin da aka kai bayan sulhu.

Wata rawar da manyan kwamandojin suka taka shi ne wanda ya kai harin suka tilasta masa da ya maido da waɗanda ya ɗauka ba tare da an bashi ko taro ba.

Wannan ya sanya ya sako mutum ɗaya da farko ana jin kafin ranar juma’a zai sako sauran huɗun da suke hannunshi.
Majiyarmu ta tabbatar mana fulanin su suka warware matsalar harin Batsari da kansu ba tare da sa hannun kowa ba kuma ba ko kwabo kamar yadda wata majiya a karamar hukumar Batsari ta tabbatar wa Taskar Labarai.

Bincikenmu a yankin Batsari ya tabbatar Fulanin sun fara fitowa daga daji suna huɗɗa da sauran al’umma ba tare da wata tsangwama ba.
………………………………………………………………………
Taskar Labarai jarida ce mai zaman kanta dake bisa yanar gizo na www.taskarlabarai.com da sauran shafukan sada zumunta ta da yar uwata ta Turanci mai suna The Links News dake bisa yanar gizo na www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here