GWAMNATIN KANO TA KASHEWA MATASAN JIHAR NAIRA MILIYAN 30

0

GWAMNATIN KANO TA KASHEWA MATASAN JIHAR NAIRA MILIYAN 30

Daga Ibrahim Hamisu

Gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya horar da matasa 60 akan gyaran manyan Motocin daukar kaya, akan tsabar kudi Naira Miliyan 30.
Ya kuma tallafa musu da kayan aiki na Miliyoyin Nairori, a karkashin shirin nan na MATASA MADOGARA shirin da gwamnatin ta kafa don horar da matasa gyaran ababen hawa,

Matasan da adadinsu yakai 60 gwamnatin Kano ta tallafa masu ne bayan wasu daga cikinsu sun kammala karatun digiri a fannoni daban daban na ayyukan injiniya.
Sannan an horar da 34 game da gyaran injin-injin na Motoci, 5 daga ciki a fagen gyara manyan motoci, 16 sun sami horo a fagen gyaran kayayyakin Lantarki Fanka, Firji da AC, yayin da biyar suka sami horo a fagen aikin Walda.

A jawabinsa yayin bikin yaye matsan da ya gudana a Gidan Afirka, (Africa Hause) dake gidan gwamati, Gwamna Ganduje ya ce “Saboda cigaban da muka sa a gaba, za mu sake horar da wasu kwararru guda 140 wadanda za su dauki irin wannan horo na tsawon wata uku a kan gyara da kuma kula da manyan motocin haya daban-daban nau’ikan sabis na inji kamar yadda akayi na farkon.
Ganduje ya ci gaba da cewa, an kuma horar da matasa guda 150 a PAN kan injiniyoyin amfani da wayar hannu, matasa 200 kuma wannan kamfani ne ya horar da su a karkashin taimakon gwamnatin jihar Kano.
A cewarsa, cibiyoyin ba da gyaran ababen hawa da aka fi sani da MATASA MADOGARA an kafa su ne a kananan hukumomi uku na jihar, sannan ya kara da cewa yayin da Kano ta Tsakiya ke da cibiyoyi hudu, Kano ta Kudu da Kano ta Arewa suna da cibiyoyi guda uku kowanne daga cikin su yana Horaswa da Gyarawa, tare da kayan aiki na zamani, kuma yana dauke da matasa maza da mata ‘yan jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here