YAN WASA GOMA DA SUKA FI CI WA KASARSU KWALLAYE A DUNIYA

0

‘YAN WASA GOMA DA SUKA FI CI WA KASARSU KWALLAYE A DUNIYA

Daga Ibrahim Hamisu

Duk da ya ke ba kowane lokaci nahiyoyi suke gabatar da gasa ba, shi kansa kofin duniya sai shekara shida-shida a ke yinsa, amma duk da haka zaka ga akwai zakakuran yan wasan da suke taka rawa a gasar wasanni ta Nahiyoyin da suke, a cikin mutum 10 din nan da aka lissafo Cristiano Ronaldo ne kawai yake buga kwallo a halin yanzu, sauran 9 duk sunyi ritaya ritaya. ga sunayen su da kasashen da suka fito kamar haka:

1. ALI DAEI: shi ne na farko a duniya da ya ci wa kasar sa kwallaye sama da dari a duniya, dan wasan kasar Iran da yaci 109, ya fara taka Leda a shekarar 1993 inda ya yi ritaya a shekarar 2006.

2. CRISTIANO RONALDO: Dan kasar Portugal yana da kwallaye 93, tsohon Dan wasan Manchester United da Real Madrid a yanzu haka yana taka leda a Juventus , dan wasan dai har yanzu Ludayinsa na kan dawo.

3. FERENC PUSKAS: Dan kasar Hungry ya ci wa Kasar Kwallaye 84, ta taka Leda daga 1950 zuwa 1960.

4. KUNISHIGE KAMAMATO: Yana da Kwallaye 80, Dan kasar Japan, Ya taka Leda daga 1964 zuwa 1977.

5. GODFRAY CHITALU: ya na da kwallaye 79, Wanda ya fito daga Afika Dan kasar Zambiya, ya ajiye Takalmi a 1993.

6. HUSSAIN SAEED: Dan kasar Iraki ya ci kwallaye 78 daga gasar nahiyar Asiya ya ajiye takalmi a shekarar 1988.

7. PELE: Yana Shahararren dan wasan da baa taba yin irinsu ba, dan kasar Barazil ya ci wa kasar kwallaye 77, Ya halacci gasar Kofin duniya sau hudu, ya dauka sau uku.

8. SANDO KOCSIS: Dan kasar Hungry ya ci Kwallaye 75 daga Nahiyar Turai.

9. BASHAR ABDALLAH: Balarabe Dan kasar Kuwait da ya ciwa kasarsa kwallaye 75, ya yi fice daga shekarar 1990 zuwa 2000.

10. SUNIL CHHITRI: Dan kasar Indiya da ya ci kwallaye 72, da yake ke buga gasar nahiyar Asiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here