BA AN RUFE BODA BANE DON CUTARWA : INJI HUKUMAR HANA FASA KAURI TA KASA

0

BA AN RUFE BODA BANE DON CUTARWA : INJI HUKUMAR HANA FASA KAURI TA KASA

Daga Taskar Labarai

Mataimakin shugaban hukumar Fasa Kwauri ta kasa ya bayyana cewa gwamnatin Tarayya bata rufe boda ta kasar nan bane domin cutar da Al’umma ko uzurawa yan kasa, yace har yanzu boda a bude take ga duk wanda zai yi shiga da fice a halastaccen tsari da kuma cikakkiyar doka.

ACG yana magana ne a wani taron manema labari da hukumar ta kira don bayyanawa jama’a aikin ta da kuma karin haske akan wata matsala da aka samu a garin Jibia ta jihar Katsina.

ACG yace rundunar su wadda ke aiki na musamman akan wannan rufe boda an dauko su ne daga duk bangarorin tsaro da hukumomin shige da fice na kasar nan.

Yace dalilai biyu suka sanya aka rufe boda na daya kowa yasan yadda matsalar tsaro ta azzara a kasar nan, kuma da yadda bayanan sirri suka tabbatar cewa duk makaman da ake amfani dasu ana shigo dasu ta kan iyakokin kasar nan ne.

Yace miyagun da akan kama suna fadar cewa makamansu daga wajen kasar nan ake shigo dasu. Na biyu yadda ake amfani da iyakokin kasar nan ana shigo da kaya da abinci Wanda shigowar su na zama zagon kasa ga ‘yan kasuwanmu da tattalin arzikin kasar mu.

Na uku yadda ake fakewa da shigo da wasu abinci ko kaya a sako kwayoyi wadanda ke lalata tarbiyyar ‘ya’yanmu da kuma kara habaka ta’addacin da ake a cikin kasa, wadanda sai yan ta’adda sun sha kwayoyin nan suke samun karfin gwaiwa.

ACG ya kara da cewa yana rokon jama’a su basu goyon baya da hadin kai akan wannan aiki da suke na kawo cigaban kasar nan da bunkasar ta. Ya kuma ce wannan aikin musamman da ake akan iyakokin nan duk kasar ne baki daya ba Katsina ba kawai.

Akan abin ya faru a Jibia yace sun yi nadamar rasa rai da jikkata da wasu suka yi, yace rai daraja gare shi basu ji dadin abin da ya faru ba kuma zasu je asibiti su jajantawa wadanda suke kwance kuma zasu je ta’azziyyar wadanda suka rasa ransu.

Yace abin da ya faru shi ne, sun samu tabbacin wani sito da aka boye gwanjo suka je tsakiyar dare domin kwasar kayan, sun gama tsaf suna kan hanya sai wasu bata gari suka afka masu. A wajen kare kai ne, aka samu jikkata da rasa rai.
……………………………………………………………………..
Taskar Labarai jarida ce dake bisa yanar gizo a shafin www.taskarlabarai.com da kuma sauran shafukan sada zumunta na social media.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here