SAJA-MANJA ADAMUN PANSHIN’ – SHEKARU 50 BAYAN RASUWAR KYAFTIN ƊANBABA

0

‘SAJA-MANJA ADAMUN PANSHIN’ – SHEKARU 50 BAYAN RASUWAR KYAFTIN ƊANBABA

Daga Ibrahim Sheme

A rana irin ta yau a cikin 1969, wato 24 ga Satumba, Allah ya ɗau ran Kyaftin Adamu Suwa Ɗanbaba, wanda aka fi sani da suna Samanja Adamun Pankshin saboda fitacciyar waƙar da Alhaji Mamman Shata ya rera masa mai taken ‘Saja-Manja Adamun Panshin”.

Wataƙila masu bibiya ta a Facebook za su tuna da cewar na yi rubutu a kan wannan bawan Allah a ranar 1 ga Disamba, 2016 – yau kusan shekara uku kenan. To a yau ma za mu tuna da wannan gwarzon ɗan kishin ƙasa, wanda ya bada ran sa ga ci-gaban Nijeriya a matsayin ta na dunƙulalliyar ƙasa, musamman da yake a yau ne ya cika shekara 50 cur tun da ya faɗi.

A rubutun da na yi a 2016, na bayyana cewar an haifi Adamu Suwa Ɗanbaba a cikin 1931 a ƙauyen Tuwan da ke cikin ƙasar Kabwir a gundumar Pankshin ta ƙasar Filato. Ɗan ƙabilar Angas ne.

Aminin Shata ne tun a Kaduna, tun kafin ɓarkewar yaƙi. Har farauta su ke zuwa tare. Waƙar da Shatan ya yi masa na ɗauke da wasu kalamai na farauta da kuma yaƙi, kuma ta kasance ɗaya daga cikin mashahuran waƙoƙin da Shata ya yi, kamar yadda na bayyana a littafin ‘Shata Ikon Allah!’

Adamu ya na daga cikin dakarun mu da ke bakin daga a yankin gabashin ƙasar nan a lokacin Yaƙin Basasar Nijeriya.

Sai dai a rubutun da na yi, na ce, “Hmmmm… An daɗe ana kashe sojoji ba a yin komai a ƙasar nan. Haka kawai wani soja ya ɗau bindiga ya harbe Adamu Pankshin har lahira kuma har yau ba abin da aka yi!”.

Mutuwar Adamu Pankshin ta na daga cikin abubuwa da dama game da Yaƙin Basasar Nijeriya waɗanda har yau ba a amsa tambayoyin da su ka lulluɓe su ba. Shi dai, Kyaftin ne lokacin da aka kashe shi a wani barikin soja a wajen yaƙin.

Wani kurtu mai suna Patrick, wanda ɗan ƙabilar Idoma ne, shi ne ya harbe Adamu da gangan, ba bisa kuskure ba. Yadda abin ya faru shi ne Adamun ne ya yi masa faɗa, har ya sa aka kulle shi kan wani laifi da ya aikata a barikin (da ma ana zargin shi da shan wiwi).

Shi kuma Patrick da aka sake shi sai ya sunno bindiga, ba zato ba tsammani ya ɗirka wa ogan nasa, wato Adamu, ya kashe shi nan take. Da yawa sun yi zaton lallai ba don an sakaya shi a gadirun ne ya kashe hafsan soja kamar Adamu ba; akwai dai wata ƙullalliya! Don haka an kama kurtun, an gana masa azaba, har an ja shi da mota a ƙasa domin ya faɗi dalilin kisan, amma ya ƙi. Abin mamaki, awa 3 kacal bayan mutuwar Adamu a ranar, sai wani ogan su kuma ya sa bindiga ya bindige Patrick har lahira. Shi kuma ba a san hujjar sa ta yin hakan ba. Hakan ya ƙara haifar da zargin cewar akwai wata manaƙisa a lamarin.

Shugaban Ƙasa, Janar Yakubu Gowon, ya sa an binciki lamarin, amma ba inda binciken ya kai. Iyalin Adamu sun yi ittifaƙi da cewa rufa-rufa aka yi, su na cewa akwai “Idoma Mafia” a birged ɗin, kuma ‘yan Idoman su na gaba da Adamu saboda mutum ne da ake ƙauna, kuma ba ya da son rai, ya na taimakon jama’a. Kurtun da ya yi harbin dai ɗan Idoma ne, to kuma shi ma ofisan da ya kashe kurtun ɗan Idoma ne.

An yi jana’izar Adamu a Pankshin tare da cikakkiyar karramawa irin ta gwarazan sojoji, wato “with full military honours”. Amma har yau ɗin nan ba a biya iyalin shi diyyar ko N1 ba.

Kyaftin Adamu ya mutu ya bar ‘ya’ya 6 – uku mata, uku maza. Babbar su ita ce Ladi Sandra Adamu, wadda yanzu Farfesa ce a Sashen Koyon Aikin Yaɗa Labarai (Mass Communication) a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya.

A rubutun da na yi a 2016, na ce: “Adamu Pankshin… gwarzon namiji ne wanda ya kamata a karrama shi a yanzu saboda gudunmawar da ya bayar ga haɗin kan Nijeriya.” Har yanzu ina bada wannan shawarar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here