NA TABA BINCIKEN YAKUBU LADO, NA KUMA GA RAHOTON SIRRI AKAN KARATUN GWAMNAN KATSINA MASARI

0

NA TABA BINCIKEN YAKUBU LADO, NA KUMA GA RAHOTON SIRRI AKAN KARATUN GWAMNAN KATSINA MASARI

Daga Danjuma Katsina

Lokacin da sanata Yakubu Lado ya fito takarar gwamna a CPC Abdu Soja yana mataimakin shi. A wancan lokacin Hajia Jadiza Bala Usman na tare da tafiyar siyasar shi.

Anyi rubuce-rubucen korafi da zarge-zarge akan sanata Yakubu Lado, daga cikin su har da zargin ya na rubuta wata diploma ta bogi a bayanan shi kuma ya cike wasu takardun da wannan diplomar.

Ni ko a lokacin ina cikin Amintattun yaran Malam MDyusufu duk wani aikin sirri kona musamman nasa wasu ina a ciki.
Hadiza Bala Usman diya ce ga MD Yusufu sai ta kai masa maganar halin da tafiyarsu ta neman gwamnan Katsina ke a ciki.

MD Yusufu na da wata halayya duk abin da zai sanya kanshi tsundum ya kan sa ayi masa bincike mai zaman kansa, wani lokacin ya kan sa dani a irin wannan bincike.

Ina katsina ya kira ni naje Abuja ya hada mu mu uku ya bamu takardun sanata Yakubu Lado yace muyi masa binciken gaskiyar abin dake ciki.

Ni ne sakataren aikin kuma duk wani mukami wanda ake cika fom da sanya takardu sai da muka je abokan aiki na duk suna tare da wasu hukumomin tsaro ne don haka ba abin da ke mana wahalar samu, muka gama aikinmu mu ka rubuta sakamakon bincikenmu muka baiwa Maigida MD Yusufu, na san me muka gano.

Wasu jiga jigai a gwamnatin Obasanjo ba su so Alhaji Aminu Masari ya zama kakakin majalisa ba, don haka ko a lokacin sun cinno masa wutar maganar takardu, manyan mutane da yawa daga arewa sun shiga maganar don kare Masari.

Ina Abuja na raka MD Yusufu wani gida cikin wadanda akayi tafiyar dasu biyu ne kadai Allah yayi masu rasuwa. Sune MD Yusufu da Umaru Shinkafi, can ne muka iske wasu jiga-jigan sai ga shugaban kasa Obasanjo yazo gidan.

Direbobi, yara da odile-odile duk muna a cikin motoci zaune bayan wani lokaci sai shugaban kasa ya fito ya tafi, bakin suka rika fitowa, malam MD Yusufu shima ya fito yana shigowa mota ya miko mani wata ambulan da yake rike da ita yace Danjuma in muka koma gida ka duba takardun nan kayi mani takaitacen sharhi akan su.

Takardu ne, masu shafuka bakwai wanda suke kumshe da rahoto a takaice, da hukumomin tsaro suka yi ma shugaban kasa akan rikicin da kakakin majalisar kasa ke ciki na takardun makarantar sa.

Daga yadda Naji daga baya Obasanjo yazo da takardun ne ya baiwa wasu da akayi taron dasu shi ne Maigida ya bani yace inyi masa sharhi a takaice. Dama yakan bani irin wannan aikin akan wasu takardu ko littafin da aka kawo masa.

Daga wannan zaman da akayi a gidan nan maganar ta fara kasa har ta mutu a lokacin. Shugaban kasa Obasanjo yayi yunkurin ta zarce karo na ukku, amma ya samu cikas dani aka shirya taron manema labaran farko Wanda sanata Uche Chukumeriji ya gabatar a ofishin MDJ dake ginin Banex Plaza, in da yace yunkurin ta zarce gaskiya ne ya kamata ‘yan Nijeriya su farka.

Lokacin da wannan kurar ta taso, wasu na kusa da Obasanjo sun so amfani da wancan makircin na sharrin takardu akan kakakin majalisa Masari.

Su kuma masu yakar Obasanjo yaci gaba suna sane da kowane motsi na masu son tazarce suna daukar masu mataki.

Gabana aka rika wasu mitin din muna matsayin dan aike da zuba shayi ko kawo abinci daga buga takardu daga cikin mitin din ne, aka shirya cewa a roki kakakin majalisa su tada ma gwamnatin hankali da maganar tsige shugaban kasa.

MD Yusufu ya kira kakakin majalisa Alhaji Aminu Masari ya yi masa tayin su dago maganar tsige shugaban kasa koda yake kakakin majalisa bai san cewa wata hikima aka tsara ba don kare shi da majalisa daga wani makirci da aka gano. Amma amsar da ya bada kamar yadda yake rubuce a rubutattcen jawabin taro shi ne, majalisa ba zata yi wannan ba.amma zai baiwa yan majalisun cikakken yancin zabarsu da akayi.

Duk da haka an gwada ma fadar shugaban kasa cewa duk Wani yunkurin taba kakakin majalisa ko majalisa zai tunzura ‘yan majalisar su dora sanwar tsige shugaban kasa.
Obasanjo ya gano, anyi wa kakakin majalisar waccar maganar da kuma amsar da ya bayar wannan ya Sanya ya rage wasu kaimin makircin da aka so yi masa.

Obasanjo yana da rauni kuma yana da kura-kurai, amma yana da tsananin kishin kasa kuma in yaga matsala zata iya kawo targade ga kasa, ko tsaro ko kasar daya yana ajiye son ransa ya chanza salo.

A shekarun da muka yi da marigayi MD Yusufu mun san ababe, kuma anyi abubuwa damu, wasu wata rana mu fade su don tarihi wasu kuma har abada ba wanda zai sani . Domin fitowarsu na iya zama zagon kasa ga kasa.

Allah ya jikan mazan jiya Alhaji MD Yusufu Danjuma Dan jarida ne, kuma shi ne mawallafin jaridu guda biyu dake bisa yanar gizo. Jaridun sune Jaridar Taskar Labarai dake a shafin www.taskarlabarai.com da kuma The links news dake www.thelinksnews.com da sauran shafukan sada zumunta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here