Dan Jarida ya bayyana a kotu daure da ankwa

0

Dan Jarida ya bayyana a kotu daure da ankwa

Jami’an tsaro sun zo da mawallafin jaridar CrossRiverWatch cikin babbar kotun Tarayya da ke Calaber daure da ankwa yau Juma’a.

Agba Jalingo ana zargin sa ne da cin amanar kasa saboda labarin da ya bayar da ya zargi Gwamnan Jihar Cross River, Ben Ayade da karkatar da Naira miliyan 500.

Jalingo an kama shi ne tun ranar 22 ga Agusta, ya kwashe kwanaki 34 a tsare a wajen ‘yan sanda ba tare da an gurfanar da shi a gaban kotu ba.

An gurfanar da dan jaridar a gaban kotu ne bayan kururuwar da kungiyoyin rajin kare hakkin bil’adama suka fara. An kai shi gaban kotu ne ranar 25 ga watan jiya.

See also  MATASA DA SANA'ARSU

Jalingo ya bayana a gaban kotu da karfe 9:18 bisa rakiyar Wadoji hudu sanye da bakar T-shirt an rubuta “Journalism Is Not A Crime”, da kuma shudin wanda jeans.

Jalingo yana murmushi yana daga wa ‘yan jarida da suka yi cincirindo a harabar kutun hannunsa da ke daure da ankwa.

Jalingo yana tare da Jonathan Ugbal, Editan labarai na jaridar CrossRiverWatch, wanda shi kuma aka kama bisa zargin yada labaran masu zanga-zangar #RevolutionNow da aka zarga da yunkurin kifar da gwamnatin Buhari a karkashin jagorancin Sowore.

Ita dai wannan shari’ar Justice Simon Amobeda ne ke jagorantarta. Ana sa ran zai ba da belin mutanen kamar yadda Lauyoyinsu suka nema.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here