AN KARRAMA MATAIMAKIN GWAMNAN KATSINA

0

AN KARRAMA MATAIMAKIN GWAMNAN KATSINA

Mataimamakin gwamnan jihar katsina Qs. Alh Mannir Yakubu ya karbi lambar yabo da karramawa daga cibiyar masana qididdigar gine gine ta kasa wato “NATIONAL INSTITUTE OF QUANTITY SURVEYORS (NIQS)”.
An gudanar da karramawar ne a lokacin walimar murnar cikar cibiyar shekaru 50 da kafuwa a babban dakin taro na International Conference Centre dake Abuja.

Alh Mannir yakubu wanda yake memba ne a cibiyar ta “NIQS” ya jinjinama membobin cibiyar bisa kokari da jajircewa da sukeyi tare da taya juna murnar samun lambar yabo da ta karramawa daga cibiyar, tare da fatan mambobin zasu cigaba da zage damtse domin ci gaban cibiyar da kasa baki daya.
Ya kuma yabama kwamitin zartaswar cibiyar bisa namijin kokarin da sukeyi ba dare ba rana don ciyar da kasa a gaba.

See also  Mutane 21 ne aka sace ba 39 ba a Katsina

A jawabin shugaban hukumar na kasa Qs. Obafeme Onashile ya yabama membobin cibiyar da suka halarci bikin cikar shekaru hamsin da kafuwar cibiyar.

Dan Majalissa mai wakiltar kankia, kusada, ingawa a majalissar tarayya Abuja Qs. Abubakar Yahaya kusada ya yaba da namijin kokarin kwamitin zartaswar cibiyar na ciyar da cibiyar a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here