BINCIKEN NA MUSAMMAN: DAUKAR CUTAR KANJAMAU DA MATAN AURE

0

BINCIKEN NA MUSAMMAN: DAUKAR CUTAR KANJAMAU DA MATAN AURE

Daga Jaridar Taskar Labarai

Jaridun Taskar Labarai da ta Turancinta The Links News sun dau watanni biyu suna wani bincike akan maza goma da mata goma sha biyar da yara guda biyar wadanda ke dauke da cutar nan da ake lira kabari salamu Alaikum ko kuma Kanjamau.

Cutar da ake dauka ta hanyar hanyoyin shigar jini har da Jima’i na halas ko haram watau zina.
Binciken mu ya dogara ga ya ake daukar ta ne da kuma yada ta.

Wani abin mamaki da muka gano mafi yawan mazan dake dauke da wannan cuta, masu neman mata ne barkatai, amma sun fi kwarewa da neman matan aure. Watau matan da suna da aure amma saboda abin duniya ko lalacewa suna kuma neman mazan da ba nasu ba a waje.

Mutum takwas cikin homa da muka bi diddigin rayuwarsu ta neman mata kuma suna shan magani don hana yaduwar cutar a jikinsu, mazaje ne da suka dau neman mata aure wani bangaren jin dadin rayuwarsu.

Mun ji labaran mazinata da kurarsu tayi kuka amma suka dau neman matan aure wani haramtaccen al’amari a rayuwarsu suna sha’aninsu da watayarsu amma waccar cutar babu wani tabbacin suna tare da ita.

Wani ma daga cikin irin wadannan mutane yayi ma jaridun ikirarin cewa laifin shi tsakanin sa da Allah ne, baya neman yara kanana baya neman wadda ke cikin gida uwaye na kula da ita baya neman matan aure, amma duk matar da shigo kasuwa ta baje hajarta to in ta yi masa zai saka kudinsa a kasuwancin nata.

Yace yana jin kila shi yasa Allah ya kiyaye shi daga duk wata cuta ta neman mata, ya kuma kare masa dukiyar shi yace yasan abin da yake laifi ne amma yana neman gafara ga Allah kuma yana fatan bari.

Wannan bincike namu ya sanya har muka fara nazarin ko daukar kanjamau ta neman mata na da alaka da zina ta shiga babban hakki? Kamar hakkin aure?

Jaridun sun tace da tantance binciken nasu kafin fitar da sakamakon rahoton cikakke nan gaba kadan. Mun boye sunaye da gari na wadanda jaridar tayi magana da bincike akai mun kuma samu hadin kan hatta wasu malaman lafiya na wannan sashen bisa amana da a fitar da abin da zai taimaki Al umma.

Jaridun yanzu haka suna gabatar da bincike kala-kala akan abubuwa daban, Wanda duk suka kammala zasu sake shi don ilmantar da Al umma.
………………………………………………………………………….
Taskar labarai da the links news jaridu ne a bisa yanar gizo da sauran shafukan sada zumunta, masu zaman kansu kuma suna da cikakkiyar rijista ta kasa ana iya samunsu a www.taskarlabarai.com da kuma www.thelinksnews.com da bisa lambar whatsapp ko Kira ta 07043777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here