YAU SHUGABAN KASA BUHARI ZAI TAYA GWAMNAN KATSINA MASARI MURNAR NASARAR DA YA SAMU A KOTU

0

YAU SHUGABAN KASA BUHARI ZAI TAYA GWAMNAN KATSINA MASARI MURNAR NASARAR DA YA SAMU A KOTU
daga taskar labarai
Jaridun taskar labarai da The links news sun dau sati guda suna bincike akan kome ya Sanya shugaban Muhammad Buhari bai taya gwamnan katsina Alhaji Aminu Bello masari murnar nasarar da ya samu a kotu ba.
Mun bi duk kafofin labarai muka gano cewa duk nasarar da aka samu a kotu shugaban kasa kan fitar da sanarwar murna ga Wanda ya samu nasarar Dan jam iyyar APC ta hanyar mai bashi shawara akan watsa labarai Alhaji Garba shehu.
Jaridun sun tabbatar da cewa wannan tsohuwar al ada ce a daga fadar shugaban kasa.
Tambaya me ya Sanya wannan sakon taya murnar ba a fitar akan gwamnan katsina ba?
Bayan kammala binciken mu.mun tura sakon tambaya ga Alhaji Garba shehu kakakin fadar shugaban kasa akan ya fada ma jaridun ko me ya Sanya. Ba a fitar da sakon taya murna ba akan gwamnan katsina masari. ba ?
Garba shehu Wanda ya San da zaman jaridun mu yana kuma bin labaranta da binciken musamman da su keyi.
Ya bada amsa kamar haka. Malam Danjuma munga sakonka. Kuma a yau za a fitar da sanarwar taya gwamnan katsina masari murna .insha Allah .mun gode .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here