BUƊE CIBIYAR SADARWA TA GAGGAWA (112) NA BUKATAR SABON LALE DA KULAWA

0

BUƊE CIBIYAR SADARWA TA GAGGAWA (112) NA BUKATAR SABON LALE DA KULAWA

daga HK Yar adua

Ayyukan da al’ummar Najeriya suke fata musamman daga wannan gwamnati wadda talakawan Najeria su kai tsaye ganin ta sake ɗarewa karagar mulki sune ayyuka masu ɗorewa. Daga cikin ayyukan da Sabon Ministan Sadarwa Dr. Isa Ali Pantami ya ƙaddamar akwai buɗe cibiyar SADARWA TA GAGGAWA (Emergency Communication Centers) wadda aka yi a ranar 24/09/2019 a jihar Katsina, wanda al’umma da dama sun yi maraba da nuna farin cikin su da wannan aiki, da kuma fatan aikin ya mai ɗorewa ne musamman ya fito daga ofishin Dr. Pantamy Malami masanin Allah.

A ranar da aka ƙaddamar da wannan aiki, na yi ƙoƙarin kiran lambar ta gaggawa wadda ita ce Dr. Isah Ali Pantamy (Ministan Sadarwa) ya ƙaddamar, a lokacin da na kira lambar 112 ta shiga mu ka yi magana da ma’aikacin da ke amsar kiran gaggawar na ce mashi da man na kira ne domin in tabbatar da cewa lambar na aiki, ma’aikacin ya tabbatar min da suna aiki a tsawon sa’annin kwana (24 hours) ya kuma ƙara min da cewa idan ana cikin yanayi na rashin lafiya ko gobara ko ɓarayi sun afko ma mutum duk ana iya kiransu domin suna da alaƙa ta kai tsaye da jami’an kiwon lafiya, ‘Yan Sanda, Yan Kwana-kwana da jami’an Road Safety dss.

See also  BARA GURBIN 'YAN JAM'IYYAR PDP NE KAƊAI KE CANZA SHEƘA ZUWA WASU JAM'IYYU IN JI MAƘARFI

Bayan kwanaki da ɓude ma’aikatar lamurra sai su ka fara canza wa ta yadda ko ka kira lambar ba ta shiga kwata-kwata, a binciken da mu ka yi mun gano cewa matsalar dake fuskantar cibiyar na da alaka ga rashin wadattaun kayan aiki, da kuma man diesel domin kunna ma injin ɗin da ke bada wuta ga cibiyar kamar yadda binciken mu ya tabbatar, yanzun haka da nike rubutun nan sai da na jarraba kiran lambar amman ba ta shiga kamar yadda hoton nan ya nuna.

Kan haka ne mu ke so mu isar da wannan saƙo ga ministan sadarwa Dr. Isa Ali Pantami cewa ayyuka irin waɗanananɗ wanda aka kashe maƙudan kuɗaɗe don ganin an inganta rayuwar al’umma musamman yadda lamarin tsaro ya zama barazana ga al’umma amman ace an kashe kuɗin a banza. Don haka muna kira da ayi bincike domin ganin wannan aiki ya cigaba.

Hassan Kabir Yaradua
Ya rubuto daga Hk Yaradua Islamic Media, Katsina.
08030524842
08/10/19

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here