Zaben 2019: Rawar Da Kungiyar BCO Ta Taka A Nasarar Buhari

0
437

Zaben 2019: Rawar Da Kungiyar BCO Ta Taka A Nasarar Buhari

Daga Muhammad Abubakar
Tabbas za a iya cewa, kungiyar kamfen ta Buhari, wacce a ka fi sani da kungiyar BCO ta taka muhimmiyar rawa a nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC suka samu a zaben 2019 da ya gabata.
Kungiyar ta BCO, ta samu wadannan nasarori ne duba da irin zakakurai kuma hazikai da ta ke da su a cikinta. Musamman Daraktan Sadarwa da Tsare-tsarenta, wato Mallam Gidado Ibrahim. Mutum ne da ya sadaukar da komi nasa wurin ganin sun yi sharar fage ga nasarar jam’iyyar APC a matakin kasa da jihohi. Kungiyar ta yi aiki mai zurfi a fannoni daban-daban, ciki har da nazartar tuggu da manakisar babbar jam’iyyar adawa ta PDP, tare da samar da hanyoyin dakile su.
BCO kungiya ce da ta yi tsayin daka a turbar da a ka samar da ita domin shi. Wannan kuwa ya hada da wayar da kan al’umma ‘yan Nijeriya game da natijar sake zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a karo na biyu. Har sai da ta kai, ‘yan Nijeriya sun fi gamsuwa da sauraron me kungiyar BCO za ta ce, idan wani al’amari ya faru.
Wannan aminci da BCO ta samu a zukatan ‘yan Nijeriya ya samo asali ne daga fadin gaskiya, da kokari wurin kiyaye mutumtaka da hakki a yayin da suke gudanar da ayyukansu. Kungiyar ba ta taba busar iska ta saki karairayi da nufin neman suna ko tausayawa daga ‘yan Nijeriya ba. Ta kan yi amfani da kwarewa da basira wurin tace bayananta kafin ta fitar da su ga al’umma.
A yayin da ranar 29 ga watan Mayu ke fuskanto mu, ranar da za a yi bukin rantsarwa a karo na biyu ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yana da kyau a yaba da irin gudummawar da wannan kungiya ta bayar a aikin kamfen din Shugaban Kasan.
Tun bayan da jam’iyyar PDP ta ayyana Atiku a matsayin dan takarar Shugaban Kasa a karkashin inuwar jam’iyyar, sai BCO ta fitar da takardar manema labarai, inda ta bayyana jin dadinta ga tsayar da Atiku a matsayin dan takara, a cewar kungiyar, wannan zai zama abu mai sauki ga kamfen dinsu. Kungiyar BCO ta kafa hujja da cewa, matukar har PDP ba ta zau darasi daga kurakurenta na shekaru 16 da suka shude ba, wanda hakan ya sa ta aminta da takarar Atiku (daya daga cikin shugabanni a tsawon shekaru 16) toh babu yadda za a yi ‘yan Nijeriya su natsu da tsarinsu.
Haka kuwa a ka yi, domin lamarin a bayyane yake, ‘yan Nijeriya sun cire
daga PDP da duk wani wanda ya taba shugabanci a jam’iyyar. Saboda a tsawon shekaru 16 da jam’iyyar ta yi tana mulki banda wahala da azaba babu abin da jama’a suka sha.
Zuwan Atiku a matsayin dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ya karawa BCO karfin gwiwa a yakin neman zabenta. Sai dai kuma, wannan ya tilastawa kungiyar ta BCO kara jajircewa a kan aikin nasu. Domin ko ba komi, sun san cewa Atiku tsohon hannu ne, wanda da shi PDP ta somo mulkinta tun a shekarar 1999. Duk wani tuggu da makarkashiyar mulki ya san da su.
Daga cikin kalubalen da BCO ta fara fuskanta akwai batun cewa, Alhaji Atiku Abubakar da tawagar kamfen dinsa sun kware matuka a harkar farfagandar siyasa. Haka kuma daga cikin shika-shikan PDP akwai yarfe da kazafi wanda suka yi ta yi wa Shugaba Buhari da jam’iyyar APC.
Sai dai, rashin sa’ar da PDP da dan takararta Atiku suka yi, sun hadu da gogaggun masana farfaganda da tuggun siyasa. Domin kuwa, Kungiyar BCO ta tsaya cik, ta yi ta warware duk wata farfaganda da tuggu da jam’iyyar PDP ta kulla. Wanda ta kai, ita kanta PDP din sai da ta tsorata da zimmar BCO.
BCO ce kadai kungiyar da ta sako Atiku da PDP a gaba, ta yadda sai da ta kai jam’iyyar ta PDP da Atiku suna shakkar sakin magana yadda suka ga dama, idan za su yi kazafi ko karya, ko farfagandar da yarfe, sai sun ciza sun furza tukunna, saboda tsoron martanin BCO.
Har sai da aka zo lokacin da Jam’iyyar PDP ta yi sanyin jiki da sakin maganganu, a wannan lokacin ne kuma BCO ta fara sakin bayanai ingantattu kan gazawar PDP da dan takararta Atiku.
Daga cikin abin da BCO ta yi wurin tabbatar da nasarar APC da Buhari, akwai yawo zuwa jihohin Nijeriya da kungiyar ta shirya, wanda ta rika shirya zama da taruka na musamman da manyan mutane a garuruwa, ciki har da sarakuna da sauransu. Wannan salon yakin neman zabe na BCO ya yi matukar taimakawa Buhari.
Ba a nan kawai kungiyar ta BCO ta tsaya ba, tana da kyakkyawan alaka mai karfi a tsakaninta da kafafen watsa labarai, wanda wannan ma ba karamar nasara ba ce.
Tarihin tafiyar BCO da nasarorinta ba za su taba kammaluwa ba har sai an sako Daraktan sadarwa da tsare-tsaren kungiyar, wato Mallam Gidado Ibrahim. Wanda ya nuna matukar kwarewa da hazaka a yanayin aikinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here