AHMAD DANGIWA YASHA WAHALAR SIYASA

0

AHMAD DANGIWA YASHA WAHALAR SIYASA~~~Gwamnan Katsina Masari

Daga Taskar Labarai

Gwamnan Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana Arc Ahmad Dangiwa a matsayin wani misali abin koyi a siyasa wanda yasha wahalarta yayi mata bauta ya kuma sha tsayawa takara fitar da gwani jam’iyyar da yake ma bauta tana bayar dashi, amma duk da haka bai taba juya ma jam’iyyar baya.

Gwamnan yace wannan shi ne ake kira da a da biyayya na gaskiya ga halastaccen dan jam’iyya na kwarai. Halastaccen da ga jam’iyya shi ne Wwanda ya nema ya rasa amma bai canza da’a da biyayyarsa ba.

Gwamnan yace duk wanda ya nema ya rasa ya fara rawa ko zafin zuciya kuma yazo yace shi mai biyayya ne fada yake da fatar baki kawai.

Gwamnan yace sun fara motsin da ya kawo su ga gwamnati tun a 2009, yace wasu daga cikin wadanda suke a cikin tafiyar akwai Ahmad Dangiwa, Dakta Mustafa Inuwa, Muntari Lawal, Dikko Radda da sauransu. Muka tsara Dangiwa da Mustafa Knuwa su rike jam’iyya.

Gwamnan yace labarin yana da tsawo da fatan wata rana wani dan cikin tafiyar ya rubuta littafin abin da ya faru don na baya su karu da ilmin cikinsa.

Gwamnan yace aka kafa shugabannin jam’iyya ni Masari ba wanda na kawo Funtua sanata Abu Ibrahim ne ya kawo kaf nan Katsina sanata Sadik ‘Yar’adua ya kawo su.

Dakta Mustafa Inuwa ya zama shugaban jam’iyya duk ‘yan takara kowa na zargin sa cewa yana tare dani shi da Ahmad Dangiwa Allah yayi har na zama dan takara kuma na zama gwamna yanzu karo na biyu.

Masari yace an shiga galan sosai da Dangiwa amma bai taba canzawa ba yana tare da jam’iyyar da kudin sa da karfinsa da kwalwarsa/don haka in naji wani ya ce wai Dangiwa kaza sai in kalle shi in yi dariya kila bai san waye shi ba ni nasan waye shi.

Gwamnan na magana ne a wani taro da akayi daren asabar 12 oktoba 2019 don karrama wasu mutane da suka taimaka ma jam:iyyar APC taci zabe. A taron an karrama mutane ciki har da gwamnan Katsina da Arc Ahmad Dangiwa da Hadiza Bala Usman da sauransu, an kuma karrama kungiyoyi ciki har da APC social Media Crew da Masari Restoration Project da sauransu.
……………………………………………………………………..
Taskar Labarai da The Links News jaridu ne masu zaman kansu da ke bisa yanar gizo da sauran shafukan sada zumunta na social media. ana samunsu a www.taskarlabarai.com da kuma www.thelinksnews.com da kuma layin whatsapp 070437777779

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here